✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Da gaske kafafun shanshani sun kai 100?

A cewar masana, rikakken shansani na iya hadiye wani karamin kwado ko tsuntsu.

Shanshani kwaro ne da ana iya gani a ko’ina, gida ko daji saboda sha’awar zamansa a wurare irin su karkashin duwatsu da bawon jikin bishiyoyi da karkashin kasa da sauransu.

Binciken masana ya nuna ana da nau’in Shanshani a doron kasa da yawansu ya kai 3,300.

Yana da kafafu birjik wadanda da su yakan yi amfani wajen tafiya da yawatawa.

Yayin da wasu ke ra’ayin kafafun Shanshani guda 100 ne dai, zance mafi karfi shi ne, bai yiwuwa a samu shansahin da kafafu 100 daidai, sai dai su haura hakan ko su gaza.

Idan ya yi girma, tsayin wannan kwaro yana kai maki 4 zuwa 300 a ma’aunin milimita, kwatankwacin inci 0.16 zuwa 12.

Shanshani na da siffofi da dabi’u masu ban al’ajabi. Ga wasu daga ciki:

* Ba a samun shanshani mai kafafu 100 daidai, sai dai 100 da doriya ko kuma kasa da 100. Kuma sun fi zama a mara, misali kamar 101, 103, 95, 97 da makamantansu.

* Mafi karancin kafafun da suke samu shi ne 15, mafi yawa kuma 191.

* Duk lokacin da wannan kwaro ya fada a tarkon manyan kwari ko tsuntsaye wadanda za su iya cinye shi, yakan sadaukar da wasu kafafuwansa don ya tsira da ransa. Sai ya bar tsuntsun da tulin kafufunsa a bakinsa, alhali ya zame jiki ya sulale.

* Bayan wasu lokuta, kafafun da ya rasa yayin faramkin wani kwaro ko tsuntusu, sukan toho su cike gurbi. Duk lokacin da aka ga wani shanshani kafafunsa wasu sun fi wasu tsayi, kafafun da ya rasa ne suke kokarin tofowa.

* Suna iya rayuwa na tsawon shekara biyar zuwa shida muddin babu abin da ya takura musu.

* Kwari ne masu cin ‘yan uwansu kwari idan dama ta samu. Kuma suna da basirar farauta.

* Yana da guba wanda idan ya harbi abun farautarsa, yakan zuba masa ya kashe ko ya nakasa shi kafin ya ci.

* A cewar masana, rikakken shansani na iya hadiye wani karamin kwado ko tsuntsu.

* Kwaro ne wanda ya fi gane ma lokutan dare.

* Da kafafunsu na gaba suke amfani wajen zuba wa abin da suka kama guba. Wannan dabi’a ce wadda kusan shanshani kadai ke da baiwarta.

* Duk da hadarin da wannan kwaro ke da shi, ba a rasa mutanen da suke kiwon sa don sha’awa.

* Bayan saka kwai mai yawa, uwar ce kan hau ta yi kwanci har zuwa lokacin kyankyashewa.

* Suna da sauri wajen tafiya. Kuma duka kafufun suna aiki yayin da suke tafiya.