✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Da hikima zan shugabanci APC ba yawan shekaru ba —Abdullahi Adamu

Jagorancin jam’iyya ba gasar dambe ba ce ko ta tsere, ana amfani ne da hukima.

Sabon shugaban jam’iyyar APC na kasa, Sanata Abdullahi Adamu wanda ya karbi ragamar jam’iyyar a ranar Laraba, ya ce zai yi amfani da hikima wajen jagoranci, ba zunzurutun karfi irin na masu kuruciya ba.

Sanata Abdullahi Adamu wanda ya ce zai yi amfani da basira ne wajen jagoranci na fadin haka ne yayin gana wa da wasu kebabbun kafofin yada labarai jim kadan bayan fara aiki a hedikwatar jam’iyyar da ke Abuja, inda ya mayar da martani ga masu yin suka a kan tasirin yawan shekaru da yake da su ga shugabanci irin na siyasa.

A cewarsa, “Ai an rage adadin shekaruna da kamar biyar idan a ka ce ni dan shekara saba’in ne, ko ma na ce da shekaru bakwai idan an bi lissafin Muhammadiyya.

“Na kuma gode wa Allah da ya tsawaita rayuwata zuwa shekarun sannan Ya hore mini kyaututuka da kuma baiwarSa a gare ni.

“Ina alfahari da shekarun musamman idan na duba yadda galibin abokaina na yarinta a makarantar firamare har zuwa jami’a, da Allah ya karbi rayuwarsu.

“Mutum ba zai taba cewa tsufa ta yi masa yawa ba, Allah Ya karbi ransa haka nan ba.

“Yin hakan tamkar aikata sabo ne, inji shi.

Sanata Abdullahi Adamu ya ce abinda yawanci masu sukarsa a kan shekarun su ka gaza ganewa, shi ne; “Ai tarin shekaru wata baiwa ce, kuma ina yi wa masu irin wannar sukar da suma Allah Ya wadata su da tsawon rai.

Sanata Abdullahi Adamu ya kuma ce jagorancin jam’iyya ba gasar dambe ba ce ko ta tsere-tsere, sai dai na basira da kuma tsare-tsare.

“Ba a zabeni don wancan ba, sai dai don samar da jagoranci mai ma’ana, wannan shi ne nake jin wadanda su ka gabatar da sunana da kuma tsayuwar daka wajen ganin na yi nasara, suka tsaya a kai,” a cewarsa.

Ya mika godiyarsa ga shugaban kasa Muhammadu Buhari tare da gwamnonin jam’iyyar wadanda ya ce “Allah Ya yi amfani da su” a lamarin, inda ya sha alwashin kai jam’iyyar zuwa tudun mun tsira.

Da yake tsokaci kan tambayar da aka yi masa a kan matsalar tsaro da kasar nan ke fama da ita a halin yanzu, tsohon gwamnan na Jihar Nasarawa ya ce za a gayyato dukkan masu ruwa da tsaki kan sha’anin tsaro, don samar da wani sabon tsari kan yadda za a tinkari lamarin.