✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Da kasashen Afirka za a soma rabon tallafin hatsin Ukraine – Erdoğan

Shuagan Kasar Turkiya, Recep Tayyip Erdoğan ya ce, za a ba da fifiko ga kasashen Afirka wajen rabon tallafin hatsi daga Ukraine don rage radadin…

Shuagan Kasar Turkiya, Recep Tayyip Erdoğan ya ce, za a ba da fifiko ga kasashen Afirka wajen rabon tallafin hatsi daga Ukraine don rage radadin yunwa.

Erdogan ya shaida wa mambobin jam’iyyarsu cewa, Shugaban Rasha Vladimir Putin ne ya ba da shawarar yayin rabon hatsin, a ba da fifiko ga kasashen na Afirka.

Ya ce kashen Afirka irin su Somalia da Djibouti da kuma Sudan za su kasance kan gaba wajen samun tallafin.

Erdoğan ya kara da cewa, Ministan Tsaron Turkiyya, Hulusi Akar, ya taimaka wajen shawo kan kasarsa dangane da harkallar ba da tallafin hatsin.

Ministan Tsaron Turkiyya ya ce, tuni an fara rabon hatsin kamar yadda aka alkawarta.

(NAN)