✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

‘Da kyar muke numfashi bayan ambaliya ta ritsa da jirginmu’

Fasinjojin jirgi mai tafiya a karkashin sun sha da kyar bayan ambaliyar ruwan sama.

Daruruwan matafiya sun sha da kyar bayan ambaliyar ruwan sama ta ritsa da su a lokacin da suke cikin jirgi mai tafiya a karkashin kasa.

Fasinjojiin da ruwan ya malale a kasar China sun yi ta kokarin tsira da ransu bayan ruwan ya shigo jirgin yana kokarin tafiya da wasunsu.

Cikin mutanen ya duri ruwa matuka, ganin tun ruwan na ranar Talata yana kai musu kwauri ya rika karuwa har ya kawo gwiwa, zuwa kwankwso, har zuwa cibiya, kuma bai tsaya ba.

Gajeru daga cikin fasinjoji sun fi shiga cikin tsaka mai wuya — da kyar suke iya yin nishi saboda sun kusa nutsewa a cikin ruwan.

Sai da wasu fasinjoji suka yi ta taimakawa suna daga su a cikin jirgin domin su samu shakar numfashi a yayin da ake ta kokarin ganin yadda za a ceto fasinjojin jirgin karkashin kasar.

Wani bidiyo da aka yada a dandalin sadar da zumunta, ya nuna wasu fasinjojin jirgin sun yi tsaye a kan kujeru sun daga kawunansu daf da rufi.

Wasu daga cikin fasinjojin a lokacin da ruwan ke neman shanye su. (Hoto: Bon News Haiti).
Wasu daga cikin fasinjojin a lokacin da ruwan ke neman shanye su. (Hoto: Bon News Haiti).

An ga wani daga cikinsu ya yi yunkurin fasa tagar jirgin, sai kuma ya lura cewa, ruwan da ke wajen taragon ma ya fi na ciki yawa.

Wasu daga cikin fasinjojin kuma sun yi ta kiran ’yan uwa suna neman a kawo musu dauki, a yayin da wasu ke ta daukar bidiyo.

“Ba zan iya magana ba kuma! Idan ba a kawo mana dauki ba nan da minti 20 masu zuwa, daruruwan mutane za su mutu,” kamar yadda wata fasinja ta rubuta shafinta ta Weibo.

Ita ma wata fasinja mai Mis Li ta shaida wa kamfanin labaru na Elephant News cewa, “Dukkanmu mun mike tsaye, ruwa ya riga ya kawo mana guiwa.

“Gajerun cikinmu ruwan ya riga ya kawo musu wuya,” tan mai cewa da kyar mutane ke iya numfashi saboda karancin iskar cikin taragon.

Bayan kimanin sa’a guda, sai aka ga taragon ya koma cikin duhu, karancin iskar ta kara tsananta.

“Na kidime sosai, abin da ya fi tayar mini da hankali shi ne karancin iska, ba wai ruwan ba,” inji wani mutum daga cikin fasinjojin.

Bayan shafe sa’o’i cikin firgici da rashin tabbas, masu aikin ceto sun samun nasarar bude rufin taragon sun fitar da mutane.

“Mun dan bugi gilashin [rufin taragon] sai iska ta dan fara shigowa,” inji wata daga cikin fasinjojin, bayan sun tsallake rijiya da baya.

A karshe dai daruwan fasinjojin sun kubuta bayan ambaliyar ta birnin Zhengzhou, na Lardin Henan a kasar China.

Sai dai mutum 12 sun rasu a ambaliyar da ta jefa kasar cikin tashin hankali, baya ga asarar dimbin dukiya da ba a kai ga kammala tantance yawanta ba.