Daily Trust Aminiya - Da na shekara a Kano da kwaya ta zama tarihi  – Wakili
Subscribe

Kwamishinan ‘Yan Sandan Jihar Kano Muhammad Wakili

Da na shekara a Kano da kwaya ta zama tarihi  – Wakili

A kwanakin baya ne Kwamishinan ’Yan sandan  Jihar Kano Muhammad Wakil, wanda aka fi sani da ‘Singam’ ya yi ritaya daga aikin dan sanda bayan da ya kwashe shekara 35 a aikin. Bisa la’akari da yadda ya tada kura a dan takaitaccen aikinsa a Jihar Kano, musamman yadda ya rika tunkarar dillalai da masu shan kwaya, Aminiya ta tattauna da shi, inda ya bayyana cewa tuni ya fara kewar aikin dan sanda ganin cewa a yanzu ba ya da damar da zai iya kama wanda ake zargi da laifi ballantana ya “toshe” shi; domin a cewarsa babu abin da yake jin dadi a harkar aikin dan sanda illa ya kwato wa mai hakki hakkinsa:

Da farko ma, me ya ba ka sha’awa ka shiga aikin dan sanda?

Zan iya cewa ni dai na tashi ina son aikin dan sanda. Mahaifina yana ba ni labarin cewa tun ina karami ake tambayata wane aiki zan yi sai in ce dan sanda nake son yi, sai mahaifiyata ta rungume ni ta ce Allah Ya sa in zama dan sanda kamar Kam Salim. A lokacin shi ne ke rike da mukamin Sufeto-Janar na ’Yan sandan Najeriya. Tun dga wancan lokaci na dora raina a kan wannan aiki har Allah Ya sa na fara kuma ga shi Allah Ya kawo mu lokacin da na ajiye aikin.

Ga shi ka yi ritaya daga aikin dan sanda a wannan lokaci, me za ka bayyana a matsayin nasarar da ka samu a aikin?

Ai suna da yawa sai dai mu dan kira wasu daga ciki ke nan. A baya-bayan nan yadda muka kama katan 300 na kwayar Tiramol kadai ya ishe mu nasara. Haka yadda aka yi babban zabe lafiya a Jihar Kano karkashin jagorancina, wannan ma babbar nasara ce. Sannan abin da nake jin dadi a wanan aiki shi ne yadda zan karbi hakki daga wurin azzalumi in damka shi ga mai shi, wannan shi ne babbar nasara da jin dadi a aikin gaba daya. Sannan ina jin dadin in kama mai laifi in toshe shi. Wannan yana daga cikin abin da zan yi kewa a aikin dan sanda. A ce yau ni zan ga mai aikata laifi amma ba zan iya kama shi ba, sai dai ni ma in kai shi gaba. Idan an yi sa’a an samu dan sanda nagari ya yi masa abin da ya dace, idan kuma aka samu akasin haka shi ke nan.

Lokacin da ka zo Jihar Kano ka yi alkawarin za ka kakkabe harkar shan miyagun kwayoyi. Me ya sa ka dauki wannan bangre kuma shin an samu kaiwa ga gaci?

Zan iya cewa tun muna yara muna sauraren wakar Danmaraya Jos, wacce ya yi gargadi a kan shan kwaya. To tun daga wancan lokaci abin ya zauna mini a rai, cewa kwaya ba ta da kyau. Lokacin da na fara aikin dan sanda kuma sai na fahimci cewa duk kusan laifuffukan da ake aikatawa ana yin su ne dalilin shan kwaya. Daga baya-baya nan kuma sai abin ya zama kamar annoba, kowa kukan kwaya yake yi, gwamnati da talakawa kowa kukanta yake yi. Don haka sai na ga cewa babban abin da za a yi a hana aikata laifi to a raba jama’a da tu’ammali da kwaya. Abin da yake damuna game da kwaya shi ne, su mutanen da ke sayarwa suna karbar kudinsu su bar al’umma suna ta tambele. Sannan ita wannan kwaya tana cutar da ’ya’yanmu, inda suke zama ’yan kwaya, ba su da wata rayuwa a nan gaba.

Alhamdu lillahi, iya zamana a Jihar Kano ina ganin mun dan samu nasara, duk da cewa ba mu kai inda muke so mu kai ba. Domin idan kika dauki irin yadda muka fara kamen kwaya a Jihar Kano, ke kanki kin san mun dan taba wani abu. Kuma na tabbata da na samu karin shekara daya a Kano, to da neman allura a dami za a yi wa kwaya, domin sai mun yi kokarin ganin mun kai ga kame masu kawo wadannan kwayoyi cikin jihar.

Wane gibi kake tunani yin ritayarka zai haifar a aikin dan sanda?

Babu wani gibi, domin ai aikin tun kafin mu zo ake yin sa, kuma ko mun bari za a ci gaba. Don haka don na tafi babu abin da za a daina, aikin dan sanda zai ci gaba. Babu wani da zai tsaya illa kawai ni ne zan yi kewar aikin dan sanda, don ba zan samu damar kama mai laifi ba. Amma a da zan iya kama mai laifi in toshe shi. Idan an yi sa’a an samu dan sanda nagari ya yi abin da ya dace, idan kuma aka samu akasin haka, kin ga akwai matsala.

Idan da za a ba ka dama ka gyara aikin dan sanda me za ka yi?

Wannan abu ne da aka sani, domin kwararru sun yi rubuce-rubuce a kan hanyoyin da za a bi a gyara aikin dan sanda, sai dai aiki da abin ne ya gagara. Amma duk da haka ina ganin da farko dan sanda yana bukatar a kula da hakkinsa. Sannan a rika ba shi horo a kai-a kai. Haka kuma akwai bukatar gwamnati ta kara daukar ’yan sanda domin yawan ’yan sanda ya yi kadan a kasar nan. Muna ganin idan aka gyara harkar shugabanci to za a samu tsabta a aikin. Shugabanci shi ne komai, shugaba ne kawai zai gyara komai. Idan aka samu tsayayyen shugaba to zai iya juya tare da gyara aikin dan sanda. Kai ba aikin dan sanda kawai ba, idan aka samu tsayayyen shugaba to zai iya juya kasar nan gaba daya. Don haka shugabanci yana da muhimmanci kwarai da gaske.

Kwamishina Muhammad Wakili (mai ritaya), a lokacin da yake bakin aiki

Wacce shawara kake da ita ga ’yan sanda?

Abu uku ne; su ji tsoron Allah, su yi gaskiya, su yi adalci.

Wannan ba ga dan sanda kawai ba, kowane aiki mutum yake yi idan har ya dauki wannan gwadaben, to zai yi nasara zai kuma gama lafiya. Mahaifina kullum yana yi mini nasiha da yin gaskiya a aiki, inda yakan ce “Muhammad mun shiga aiki dan sanda ne don mu yi adalci mu yi gaskiya. Ita gaskiya ka fade ta ko a kan makiyinka ne.”

Wane sako kake da shi ga al’ummar Jihar Kano?

Jama’ar Jihar Kano sun nuna min kauna, kodayake lamarina da mutanen Kano ikon Allah ne. Ba wanda zai iya fadin cewa ga dalili, amma dai na san ni yanzu ina jin kaina a matsayin dan Kano, domin ina tunanin ko takara na fito zan iya kayar da dan asalin Kano. Ita kuma dama Kano ta gaji hakan ta kuma saba yi. Ina godiya ga jama’ar Jihar Kano, godiya mai tarin yawa.

Abu na biyu shi ne, mutanen Kano tun iyaye da kakanni suna da addu’a, domin Kano ba ta kai inda take haka kawai ba, sai da ya kasance mutanenta suka yi mata aiki kwarai da gaske. Mutanem Kano kuma suna da jajircewa da kwazo da adalci. Wannan ne ya sa garin ya bunkasa. Ina kira ga Kanawa su ci gaba da jajircewar da suke yi a kan ba su son zalunci da mugunta.

… Abin da ’yan sanda suke fadi a kansa

Kakakin Rundunar ’Yan sandan Jihar Kano, DSP Abdullahi Haruna, ya bayyana tsohon Kwamishinan ’Yan sanda Muhamamd Wakili a matsyain jajirtaccen ma’aikaci, wanda ba ya da tsoro. “Iya tsawon zamana a aikin dan sanda, ban taba ganin mutumin da yake aiki bisa tsari da bin ka’idar aikin kamar CP Wakili ba. Shi bai san wani abu gajiya ba. Yakan yi aiki daga safe har dare ba tare da ya nuna gajiya ba. Dan zaman da na yi da shi, na karu sosai ta fuskar aiki, domin na san abubuwa da dama da a da ban sani ba. Gaskiya na ji dadin zama da shi.

Idan kika dauki banagren hali kuma, shi mutum ne marar tsoro, mai gaskiya. Yana iya kallonka ya gaya maka gaskiya komai dacinta. Kuma yana tausaya wa na kasa da shi. Idan kana son ka ga bacin ransa to a kawo masa kukan wani babba ya cuci na kasa da shi.”

Mas’ud Mohammed dan sanda ne kuma daya ne daga cikin ma’aikatan Ofishin Hulda da Jama’a na Rundunar ’Yan sandan Jihar Kano. Ya bayyana tsohon Kwamishinnan a matsayin wanda ya san aikinsa. Haka kuma shi mutum ne mai adalci. “A gaskiya tsawon zaman da muka yi da shi mun fahimci cewa shi mutum ne da ya san aikinsa kwarai da gaske. Haka kuma mutum ne mai adalci. Ba ya so ya ga an danne hakkin na kasa. Kuma duk da cewa shi mutum ne da ba ya son raini amma hakan bai hana shi yin mu’amala da ma’aikatansa har ma su yi wasa da dariya ba. Ma’ana dai shi mutum ne mai sakin fuska.” inji shi.

More Stories