Da sana’ar gyaran waya nake biya wa ’ya’yana kudin makaranta – Maryam Usman | Aminiya

Da sana’ar gyaran waya nake biya wa ’ya’yana kudin makaranta – Maryam Usman

    Bashir Isah
Gyaran waya sana’a ce da aka fi sanin maza da ita. Amma Hajiya Maryam Usman, wata mazauniyar garin Keffi, a jihar Nasarawa ta shiga wannan sana’ar.
 
A wannan hirar da ta yi da Aminiya, ta bayyana yadda ta koya, da kuma irin alheran da ta ke samu a cikinta.