✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Da sayen fom din 2023 gara ku biya diyyar fasinjojin jirgin kasa —Gumi

Gumi ya bayyana takaici kan yadda aka karkata wajen sayen fom din takara maimakon a ceto mutane da kudaden

Mashahurim malamin Musulunci a Najeriya, Sheikh Dokta Ahmad Gumi, ya shawarci Gwamntin Tarayya ta biya diyyar mutum 62 da ’yan bindiga suka yi garkuwa da su a jirgin kasan Abuja zuwa Kaduna su sako su.

Sheikh Gumi ya yi wannan kira ne a wurin taron addu’ar neman kubutar fasinjojin jirgin, wanda kungiyar Jam’iyyar Matan Arewa ta shirya a Kaduna ranar Alhamis.

Sheik Gumi ya ce, “Ku duba, mutane sun kashe Naira biliyan 25 wajen sayen fom din tsayawa takara, maimakon su fanshi talakawan da ba su da kudin fansar kansu.

“Duk abin da (masu garkuwa da fasinjoijn jirgin kasan) suke so a ba su, domin su saki mutanen nan.

“Za a iya mu’amala da su (’yan bindigar) yadda suke so, saboda suna tsare da akwai mutanen, dole a yi hattara don kada su cutar da mutanen da ke wurinsu,” inji shi.

A ranar 28 ga watan Maris, 2022, ne ’yan bindiga da ake zargin mayakan kungiyar Ansaru ne, suka dasa bom wa jirgin kasan bom a kan titinsa.

A lokacin harin na dare, maharan sun kashe mutum tara, suka yi garkuwa da mata da kananan yara da maza 62, baya ga wadadna suka jikkata.

Kawo yanzu, mutum biyu ne kacal ’yan ta’addar suka sako.

Bayan wata daya da sace mutanen, ’yan ta’addar sun saki hotunan mutanen da kuma hoton jiririyar da daya daga cikin fasinjojin jirign ta haifa a hannunsu.

A bangaren gwamnati, ta bayyana cewa tana yin duk mai yiwuwa na ganin cewa an sako fasinjojin jirgin cikin koshin laifya.