✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Da ya kashe uba a wurin gwada maganin bindiga

Magidancin da ya sha maganin bindiga ya dora bindigarsa ce a cikinsa sannan ya tursasa wa dansa mai shekara 19 ya harba ta.

Wani dan banga ya bakunci lahira a yayin da yake gwada maganin bindiga a Jihar Adamawa.

Magidancin da ya sha maganin bindiga ya dora bindigarsa ce a cikinsa sannan ya tursasa wa dansa mai shekara 19 ya harba ta.

Harba bindigar da dan ya yi ke da wuya ta tashi da dan uban, ta kuma yi sanadiyyar mutuwarsa.

Kakakin ’yan sanda na Jihar Adamawa, SP Suleiman Yahaya Nguroje, ya shaida mana cewa lamarin ya faru ne ranar Alhamis a Karamar Hukumar Jada ta jihar.

Jami’in ya ce suna gudanar da bincike kuma duk wanda ke da hannu a cikin lamarin zai fuskanci hukunci.

Ya kuma yi kira ga jama’a da su guji amfani da makamai, wadanda ke da izinin mallakar su kuma su tabbata sun kiyaye ka’idoijin kariyar rayuwarsu da ta wasu.