Daily Trust Aminiya - Da ya kashe ubansa saboda naman kaza

Da ya kashe ubansa saboda naman kaza

Wani matashi mai shekara 26 a duniya ya shiga hannun ’yan sanda bayan ya kashe mahaifinsa saboda naman kaza.

Matashin ya bayyana wa ’yan sanda cewa ya kashe mahaifin nasa ne bayan mahaifin ya ba wa kaninsa naman kaza mai yawa, shi kuma ya ba shi kan kaza a matsayin rabonsa.

A cewar matashin, mahaifin nasa ya umarce shi da yanka wa kaninsa mai shekara bakwai kaza don faranta masa rai, “Bayan na yanka kazar, kanta kawai aka dauka aka ba ni, hakan ne ya sa na kashe mahaifina.”

Da ta ke bayani bayan kama matshin, kakakin ’yan sandan jihar Ondo, Funmilayo Odunlami, ta ce matashin ya bar gida tare da mahaifinsa da nufin zuwa gona a ranar 9 ga watan Satumba, amma bai dawo tare da shi ba.

Daga bisani aka gano cewa ya aika mahaifin nasa lahira, shi ne aka kai kara hedikwatar ’yan sandan jihar da ke Akure, don da gudanar da bincike.

DSP Odunlami ta kara da cewa matashin ya amsa laifin kisan mahaifin nasa kuma za a mika shi zuwa kotu da zarar an kammala bincike.

Karin Labarai