Da yawan ’yan APC ba su iya mulki ba – Dalung | Aminiya

Da yawan ’yan APC ba su iya mulki ba – Dalung

    Abdullahi Abubakar Umar

Tsohon Ministan Matasa da Wasanni a gwamnatin Shugaba Buhari, Solomon Dalung ya ce da yawa daga cikin masu rike da mukamai a APC ba su san yadda ake gudanar da mulki ba.

Ya bayyana hakan ne a wani bidiyo da ya wallafa a shafinsa na Facebook  yana mai nuna rashin jin dadinsa da yadda al’amura ke tafiya a kasar sakamakon rashin iya shugabancinsu.

Tsohon Ministan ya ce da yawa daga cikin shugabannin da aka zabe su tare da Shugaba Buharin basu cancanci zama shugabanin ba, kawai guguwar canjin ce ta sanya aka zabe su.

Solomon Dalung ya dora alhakin halin da ake ciki a kasar nan akan rashin kwarewar  wadannan shugabannin na gwamnatin APC.

Sai dai anyi yunkurin alakanta bayaninsa da yanayin da ya tsinci kansa na rashin mukamin nasa a yanzu,  amma ya yi martani da cewa ko kadan ba hakan bane kawai yana tausayawa jama’w halin da ake ciki a kasar na tsadar rayuwa da yunwa.

Har ila yau, tsohon Ministan ya ce ya samar da ci gaba sosai a Ma’aikatarsa  lokacin da yake matsayin minista.