Daily Trust Aminiya - DAF ta kashe mutum 4 a wani hadari
Subscribe

DAF ta kashe mutum 4 a wani hadari

Wata babbar mota kirar DAF ta kashe mutum 4 a  wani hatsarin mota da ya ritsa da su a kan titin Ijebu-Ode a Jihar Ogun.

Hadarin ya faru ne a ranar Asabar, inda mutum hudun  suka rasu sannan wasu biyu suka jikkata.

Kakakin kungiyar manyan mototci (TRACE) ma jihar, Babatunde Akinbiyi ya tabbatar da faruwar lamarin.

Ya ce karamar motar na kan hanyarta ta zuwa Ibadan ne yayin da DAF din ta kwace kuma ta murkushe su nan take.

Fasinja biyu ciki har da mace da direban motar take suka mutu, sai mutum biyu da suka ji rauni.

An garzaya da gawar wadanda suka rasun da kuma wanda suka ji raunin zuwa Babban Asibitin Ijebu-Ode.

Akinbiyi ya ja kunnen direbobi da ke tukin ganganci da su daina.

Seni Ogunyemi, shugaban kungiyar direbobin ya jajanta wa iyalan wanda hadarin ya yi sanadin mutuwarsu.

More Stories