DAGA LARABA: Asalin ta’addanci a Zamfara | Aminiya

DAGA LARABA: Asalin ta’addanci a Zamfara

    Halima Djimrao da Muhammad Auwal Suleiman

Domin sauke shirin latsa nan

Jihar Zamfara ta yi suna a duniya a shekarar 2000, sanadiyyar  kaddamar da shari’ar Musulunci.

Jama’a sunyi ta zancen Jihar da sa albarka, suna kuma kallon ta a matsayin wani wuri da za a samu wanzuwar adalci saboda abinda ake sa ran wannan sabon tsarin mulkin zai tabbatar.

Sai dai a baya-bayanan, Jihar ta tsinci kanta a bakin jama’a a wannan karon ana tir da abinda ke fitowa na ta’addanci da duk wani irin rashin mutunci da mai tunani zai tunano.

Daga ina wannan matsala ta samo asali?

Su wa ake zargi da shuka wannan bala’i da ya addabi yankin Arewa baki daya?

Shirin Daga Laraba na wannan lokaci ya binciko wurinda gizo ke saka.