DAGA LARABA: ‘Ina Sayar Da Kwalaba 1,000 Na ‘Kurkura’ a Mako A Zariya’ | Aminiya

DAGA LARABA: ‘Ina Sayar Da Kwalaba 1,000 Na ‘Kurkura’ a Mako A Zariya’

    Halima Djimrao da Muhammad Auwal Suleiman

Domin sauke shirin kai tsaye, latsa nan

Shin da gaske ne ‘Kurkura’ na maganin basir, ko dai shigo-shigo ba zurfi ake yi wa jama’a su fara shaye-shaye?

Kurkura wani magani mai guba da kuma sa maye nan take idan an zuba shi a baki.

Sai dai kuma duk da haka, yana ci gaba da samun kasuwa a tsakanin jama’a musamman a Arewacin Najeriya da sunan maganin basir da karin kuzari.

Shirin Daga Laraba na wannan makon ya yi wa wannan batu duba na musamman ta hanyar tattaunawa da masu sayarwa, masu sha da kuma likitoci.