DAGA LARABA: Tashin Hankalin Da Samari Ke Ciki Amma Suke Boyewa | Aminiya

DAGA LARABA: Tashin Hankalin Da Samari Ke Ciki Amma Suke Boyewa

    Halima Djimrao da Muhammad Auwal Suleiman

Domin sauke shirin kai tsaye, latsa nan

Samari na daga cikin mutanen da ba a cika damuwa a san abin da ke ci musu tuwo a kwarya ba.

Amma shin kun san irin mawuyacin halin da matasa maza ke ciki kuwa?

Akan dauka cewa halin da suke ciki ba abin damuwa ba ne, kuma bai dace su nuna gazawarsu ba, ballantana har su saki jiki su nema ko a ba su shawara kan matsalolin da ke addabar rayuwarsu.

Shirin Daga Laraba na wannan mako ya yi nazari mai zurfi dangane da halin da samarin ke ciki, kuma suke boyewa.

A yi sauraro lafiya.