DAGA LARABA: Yadda Ake Gane Labaran Karya | Aminiya

DAGA LARABA: Yadda Ake Gane Labaran Karya

    Halima Djimrao da Muhammad Auwal Suleiman

Domin sauke shirin latsa nan

Ta wace hanya mutum zai gane labarin karya a kafar intanet ko kuma a kafofin sada zumunta?

Wani lokaci bambance labaran karya abu ne mai sarkakiya ta yadda hatta amintattun kafafen yada labarai kan fada a tarko,  su dauke su a matsayin sahihan labarai.

Tambayar da ke yawan ci wa jama’a da dama tuwo a kwarya ita ce, ta yaya mutum zai gane labarin karya?

Shirin Daga Laraba na tafe da bayanan hanyoyin gane labaran karya da zarar an yi ido hudu da su.