DAGA LARABA: Yadda ’Yan Siyasa Ke Yada Labaran Karya Don Su Ci Zabe | Aminiya

DAGA LARABA: Yadda ’Yan Siyasa Ke Yada Labaran Karya Don Su Ci Zabe

    Muhammad Auwal Suleiman

Domin sauke shirin latsa nan

Labaran karya sun samu wurin zama a fagen siyasa, kusan ko’ina aka leka za a iske ’yan saiya na gudanar da harkokinsu ta hanyar amfani da labaran kanzon kurege a matsayin hanyar neman magoya baya da kashe farin jinin abokan hamayya.

Shirin Daga Laraba na wannan karon ya yi nazari kan yadda ’yan siyasa ke amfani da kafafen sada zumunta wurin yada labaran bogi domin sace zukatan jama’a da kuma kayar lagon abokan hamayyarsu.