✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Dahiru Mangal ya ba dan takarar Shugaban Kasa a Nijar gudunmuwar motoci 100

Fitaccen hamshakin attajirin nan na Jihar Katsina, Alhaji Dahiru Mangal, ya ba da gudunmuwar motoci sama da dari domin tallafawa Mohamed Bazoum yakin neman zaben…

Fitaccen hamshakin attajirin nan na Jihar Katsina, Alhaji Dahiru Mangal, ya ba da gudunmuwar motoci sama da dari domin tallafawa Mohamed Bazoum yakin neman zaben kujerar shugaban kasa a Jamhuriyyar Nijar.

A wani hoton bidiyo da kamfanin PR Nigeria ya samu, an gabatar da motocin ne a Maradi, birni na biyu mafi girma a Jamhuriyyar Nijar wanda kuma shi ne garin da ke kan iyaka da ya shiga tsakanin Najeriya da makociyar kasar.

An yi wa duk motocin tambari da ‘Mohammed Bazoum, 2021’ dauke da wani hoton mai jan hankali na dan takarar shugaban kasar.

An kiyasta cewa Alhaji Dahiru Barau Mangal wanda ya kafa kamfanin jiragen sama na Max Air a shekarar 2008, babban dan kasuwa ne kuma masani wanda ya kware a kan harkokin kasuwanci, yana da dukiya wadda ta kai kusan Dala miliyan 765.

Gudunmuwar da Alhaji Mangal ya bayar za ta kara karfafa damar Mohomed Bazoum a zaben wanda ya kasance dan lelen Shugaba Issofou kuma dan takarar jam’iyyar PNDS mai mulki a kasar Nijar.

A ranar Lahadi, 27 ga watan Dasimban 2020 ne ake shirin gudanar da zaben Shugaban Kasa da na ’yan Majalisun Tarayya a kasar Nijar.

Mohamed Bazoum wanda tsohon Minista ne a Kasar, zai fafata da ’yan takara 29 ciki har da tsohon shugaban kasa Mahamane Ousmane, da tsohon Firaiminista, Seini Oumarou

Sai dai a dalilin tuhumarsa da aikata miyagun laifuka, a wannan karo an haramta wa Hama Amadou takara, wanda shi ne ya zo na biyu a wancan zaben shugaban kasar da aka gudanar