✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Dahuwar shinkafa mai launuka

Wannan girki dai ko talaka zai iya yin sa.

Barkanmu da sake haduwa da ku a cikin wannan fili namu na girke-girke. Tare da fatar ana lafiya.

A yau na kawo muku yadda ake girka shinkafa mai launi-launi wadda maigida zai ji dadin ci musamman a ranakun da ba zai fita wurin aiki ko kasuwa ba.

Ina so uwargida ta gane yadda ake irin wannan girki, kuma abu ne mai sauki wanda za ta iya yi a gidanta ba sai ta je gidan biki ba, ko gidan da ake sayar da abincin zamani.

Wannan girki dai ko talaka zai iya yin sa, domin ba wani abu mai tsada za a sa a ciki ba, sai dai in ana son a kawata shi.

Abubuwan da za a bukata:

  • Shinkafa
  • Kaza
  • Attarugu
  • Koren attarugu
  • Albasa
  • Sunadarin dandano
  • Kori
  • Tumatir
  • Launi na girki (food colour)

Yadda ake yin hadin: A tafasa shinkafa sannan a tsame a matsami a wanke da ruwa sannan a ajiye a gefe.

Bayan haka sai a silala kaza da albasa da gishiri kadan har sai ta yi laushi yadda ruwan kazar zai bushe a jikinta.

Sannan a yanka albasa da tumatir sannan a jajjaga attarugu da tafarnuwa.

Sai a zuba man gyada kadan a tukunya bayan man ya yi zafi sai a zuba albasa da tumatir da jajjagen attarugun sannan sai a dauko launi na abinci kore a zuba tare da zuba ruwa kadan.

Idan ya tafasa, sai a zuba shinkafa kadan har sai ta nuna.

A sake yin irin wannan hadin da kowane launin da ake so na abincin, sannan a zuba shinkafa ta nuna. Daga nan sai a soya kaza a dora a kai.

A ci dadi lafiya!