✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Dailin direbobin motocin daukar mai na fasa yajin aiki

Direbobin sun yi niyyar yaji ne saboda hanyoyi ba kyau da arahar dakon kaya

An bayyana dalilin bangaren Direbobin Motocin Daukar Man Fetur (PTD) na Kungiyar Ma’aikatan Man Fetur da Iskar Gas ta Najeriya (NUPENG) da Kungiyar Masu Ababen Hawa ta Kasa (NARTO) na fasa shiga yajin aikin da suka shirya yi.

Kungiyoyin sun yi niyyar yajin ne domin nuna rashin jin dadinsu da yanayin hanyoyin mota da kuma hauhawar kudin daukar kaya.

Da kungiyoyin sun afka yajin aikin aikin, da an kara shiga matsanancin halin karancin mai a fadin Najeriya.

A cewar wata sanarwa da Kamfanin Man Fetur na Kasa (NNPC) ya fitar, matakin ya biyo bayan wani taro da kungiyoyin suka yi ne da shi da kuma Hukumar Kula da Ayyukan Hako Man Fetur ta Kasa (NMDPRA) ranar Alhamis.

Sanarwar ta kuma ce yayin zaman da aka yi tsakanin NMDPRA da NNPC da PTD da NARTO da NUPENG, an warware wasu batutuwa, ciki har da batun gyaran hanyoyi.

NNPC ya ce ya bayar da bayanai a kan inda aka kwana a ayyukan gine-gine da gyare-gyaren tituna a karkashin shirin yafe wa kamfanoni masu zaman kansu wani bangare na haraji don su gina/gyara hanyoyi, sannan ya tabbatar wa kungiyoyin cewa za a yi kashe kudaden da aka ware don aikin hanyoyi 21 ta hanyar da ta dace.

“Don kawar da fargabar dukkan masu ruwa da tsaki, NNPC da kungiyoyin sun kuduri aniyar aiki tare wajen sa ido a kan gina/gyaran hanyoyin.”

Sauran Bukatu

Sun kuma tattauna bukatar sake nazari a kan kudin dakon kaya sannan kungiyoyin suka bukaci a shigar da kudin gudanarwa cikin batutuwan da aake tattaunawa a kansu.

Sun kuna ja hankali a kan halin ha’ula’i da masu motocin ke ciki bisa la’akari da yanayin da kasar ke ciki.

NMDPRA ta ce an kafa wani kwamiti wanda zai yi nazari a kudin dakon kayan, kuma PTD da NARTO da NUPENG da sauran masu ruwa da tsaki mambobi ne a cikinsa.

“Dukkan kungiyoyin sun amince da gaggauta aiki don kammala nazari a kan kudin dakon kaya tare da ba da shawara ga gwamnati”, inji NMDPRA.

Sun kuma amince su yi aiki tare don tabbatar da cewa ana raba man fetur a fadin kasar nan yadda ya kamata.

Taron ya samu halartar Shugaban PTD Salimon Oladiti da Shugaban NARTO Yusuf Othman.