✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Daily Trust na kiran masu harkar noma su ci gajiyar shafin TrustPlus

Shirin dama ce ta samun labaran sabbin dabarun zamani kan harkar noma.

Kafar yada labarai ta Daily Trust ta samar da wata kafa da za ta tattaro manoma, masu zuba jari a harkar noma da masu sha’awar harkar a cikin gida da kasashen ketare, da ke da gonaki a gida.

A kan haka ne Daily Trust ke gayyatar matasan manoma ’yan Najeriya, kungiyoyin manoma, masu zuba jari da masu sha’awar harkar su yi rajista a dandalin TrustPlus ta karamin shafinta domin samun damar yin hulda da junansu.

Shirin zai ba su damar samun labarai a kan kirkire-kirkiren zamani a bangaren noma.

A wata sanarwa da yake bayani game da manufar bullo da shirin, Babban Editan Daily Trust, Malam Naziru Mikail Abubakar, ya ce: “Yanzu manoman Najeriya na cikin mawuyacin hali. Harkar noma ba ta taba fuskantar irin wannan kalubale ba.

“Wakilan Daily Trust za su rika tuntubar su domin kawo ingantattun rahotanni kan abubuwan da ke ci wa masu harkar noma tuwo a kwarya, gami da samar musu da kafar musayar dabaru da sabbin tunani da dabarun kirkira da za su bunkasa harkar noma.

“Trust Plus wani dandali ne na makaranta labaran Daily Trust masu sha’awar irin aikin jaridarmu domin kawo ci gaban rayuwar al’umma.

“Wadanda suka yi rajista za su rika samun manyan shafukan labaranmu na Youthville+ da kuma Careerville.

A nan  za su samu damar wallafa makalolinsu, labaran da suka shafi fannin ilimi, rahotanni na musamman, samun damar koyo ko daukar aiki, da samun labaranmu ta imel.

“Mambobin kafar na iya tattaunawa ta intanet da wasu hanyoyi, baya ga wasu alfanon da za a samu.

“Wannan kafa dama ce ta kasancewa da dubbban manoma da ke amfani da hanyoyin zamani wajen bunkasa sana’arsu, yin musayar kwarewa, samun muhimman bayanai da za su taimaka wa masu harkar su yi hulda da juna, tare da samun ci gaba mai dorewa.”

Ga masu sha’awar shiga wannan kafa ta manoma, sai su cike wannan fom din.

Domin karin bayani sai a turo da sakon imel zuwa [email protected] ko sakon WhatsApp a kan +2348069903410.