✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kamfanin Daily Trust ya bude shagon sayayya na intanet

Za ku iya sayen kayayyaki masu inganci daga sassan duniya a shafin Daily Trust Store

Rukunin Kamfanin Media Trust, masu buga jaridar Daily Trust da Aminiya da Trust TV ya bude shafin sayayya ta intanet a matsayin daya daga tsare-tsarensa na tafiya daidai da zamani.

Bude shafin mai suna Daily Trust Store na daga cikin hanyoyin da kamfanin ya bullo da su na fadadawa da kuma inganta harkokinsa ta hanyar bai wa masu karatun labarai wata sabuwar damar biyan bukatunsu cikin sauki.

Babban Editan Daily Trust, Naziru Mikailu, ya bayyana cewa, shagon intanet na Daily Trust Store, “Zai rika samar da sabbin nau’ikan kayayyaki iri-iri, akai-akai kuma a kan farashi mai sauki, ga masu karatun jarida da sauran jama’a.”

“Shafin Daily Trust Store babbar dama ce da kwastomomi za su iya nema su kuma sayi duk irin hajar da suke bukata masu inganci daga ko’ina a fadin duniya, kan farashi mai sauki,” in ji Naziru.

Hukumar gudanarwar kamfanin ta bayyana a safiyar Litinin cewa shafin zai rika sayar da kayan amfanin yau da kullum iri-iri masu inganci kuma cikin tsari mai gamsarwa.

Rukunin hajojin sun hada kayan abinci da kayan laturoni da kayan gida da kayan kwalliya da kayan yara da takalma.

Sauran sun hada da na’urorin zamani da litattafai da kayan amfanin ofis da magunguna da dai sauransu.

Kamfanin Daily Trust zai  gudanar da shafin kasuwannin ne da hadin gwiwar wani kamfanin kasuwanci ta intanet mai suna Gold Citti.

Babban Edita Naziru ya kara da cewa shafin Daily Trust Store yana da bangaren taimaka wa masu yin sayayya, “da zai mayar da hankali wajen bayar da bayanai da kuma kyautata alaka da masu karatun jarida.”

Latsa nan domin shiga shafin Daily Trust Store kai tsaye.