✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Dakarun MNJTF sun kashe shugabannin ISWAP 3 a gabar Tafkin Chadi

An kashe ‘yan ta’adda da dama a harin da aka kai a Tumbum Jaki da Tumbum Gini da ke Jihar Borno.

Sojojin hadakar da ke karkashin rundunar hadin gwiwa ta MNJTF daga Najeriya, Nijar da kuma Kamaru, sun samu nasarar kashe wasu shugabannin kungiyar ISWAP uku.

Rundunar Sojojin MNJTF ta kashe shugabannin ISWAP da suka Bako Gorgore, Aba-Ibrahim da Kaka Lawan.

A hare-haren da ta tsananta kaiwa kan ‘yan ta’adda na kungiyoyin Boko Haram da ISWAP a Tafkin Chadi rundunar hadin gwiwa ta (MNJTF) ta samu nasarar hallaka manyan kwamandojin ISWAP uku a tafkin Chadi.

Majiyar nan ta Zagazola Makama ta ruwaito cewa Babban Kwamandan ISWAP Bako Gorgore;  Kwamanda Hizba, Kaka Lawan da kuma wani shugaba Aba-Ibrahim an halaka su ne bayan farmakin da sojojin sama na MNJTF suka kai musu.

Majiyar ta kara da cewa, an kuma kashe ‘yan ta’adda da dama a harin da aka kai a Tumbum Jaki da Tumbum Gini da ke Karamar Hukumar Abadam a Jihar Borno.

A cewar majiyar, dukansu kwamandojin da aka hallaka sun rike manyan mukamai na jagoranci a Wylayat na Timbuktu Triangle, kafin a nada wani Abu Aseeya a matsayin Ameerul Fiya mai kula da Dajin Sambisa.

Duk da samun galaba da ake yi a kansu baya-bayan nan, kungiyoyin ‘yan ta’addan sun ci gaba da kaddamar da hare-hare a sassa da dama na kasar da suka hada da Taraba, Adamawa, Kaduna da Kogi, wadanda kungiyar ISIS mai da’awar jihadi zaburar da su dangane kai hare-haren da su ke yi.