✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Dakarun Rasha na daf da mamaye babban birnin Ukraine

Alamu na nuna cewa burin dakarun Rasha shi ne kama shugabannin Ukraine

Rahotanni sun ce dakarun Rasha sun yi wa babban birnin Ukraine, Kyiv, tsinke suna kuma nausawa tsakiyar gari.

Mazauna birnin sun bayar da labarin jin karar harbe-harbe da fashewar bama-bamai, bayan Rasha ta kwana tana luguden wuta a kan Kyiv din.

Wasu hotunan bidiyo da aka wallafa a shafukan sadarwa na zamani sun nuna yadda bama-baman suka tarwatsa gine-gine a babban birnin.

Sai dai barnar ba ta tsaya a kan gine-gine ba – yawan mutanen da suka riga mu gidan gaskiya yana karuwa yayin da wasu suke fakewa a tashoshin jiragen kasa na karkashin kasa wasu da dama kuma suke tsallakawa zuwa Poland.

Majalisar Dinkin Duniya ta ce tuni yakin ya tilsta wa dubban daruruwan mutane tserewa daga gidajensu.

Wakilin gidan talabijin na ABC ya bayar da rahoton barkewar fada a wasu titunan birnin, yayin da jami’an soji da ’yan sanda ke mika wa fararen hula makamai ba tare da la’akari da jinsi ko shekarunsu ba.

Dakarun Rasha sun kaddamar da hare-haren ne ta ko wanne bangare, kuma tuni ma sun kwace iko da wasu muhimman wurare, cikin har da kangon tashar nukuliya ta Chernobyl.

Alamu dai na nuna  cewa burin dakarun na Rasha shi ne kama shugabannin kasar ta Ukraine.

Tuni Shugaba Volodymyr Zelenskyy ya yi jawabi yana shaida wa al’ummar kasar cewa shi ne hadafin Rasha na farko.

Rasha dai ta yi tayin hawa teburin shawarwari, amma da sharadin cewa dakarun Ukraine za su ajiye makamansu.