✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Dakarun Saudiyya sun kashe mayakan juyin juya halin Iran a Yemen

Jagororin ’yan tawaye da Iran ke goyon baya sun gamu da ajalinsu a hare-haren

Jiragen yakin rundunar kawancen kasashen Larabawa da Saudiyya ke jagoranta sun tarwatsa maboyar ’yan tawayen Houthi na kasar Yemen da kawayensu da ke samun goyon bayan gwamnatin Iran.

A ranar Alhamis ne jiragen suka rusa wasu gine-gine da ke zama matattaran jagororin sojojin juyin juya halin Iran, da kungiyar Hezbollah da na ’yan tawayen Houthi a kasar Yemen.

Luguden wutar wani yunkuri ne na rundunar kawancen da Saudiyya ke jagoranta na karya lagon ’yan tawayen Houthi da ke samun goyon bayan kasar Iran.

Jiragen yakin sun tarwatsa sansanin Al-Dulaimi da wani babban dakin ajiya a Sanaa, kamar yadda gidan talabijin na Al Arabiya ya bayar da rahoto.

Sauran wuraren da aka kai hare-haren sun hada da yankunan Dhamar, Saada, da Al-Jawf.

A safiyar Alhamis din sojoji suka kakkabo wani jirgi mara matuki da ke kokarin kai hari a filin jirgin sama na Abha da ke Lardin Asir na kasar Saudiyya.

’Yan tawayen Houthi na yawan kai wa Saudiyya hare-haren jirage marasa matuka, amma hare-haren ba su fiye kai wa ga nasara ba.