✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Dakatar da Twitter: Najeriya ta gayyaci jakadun kasashen Yamma

Gwamnatin Najeriya ta gayyaci jakadun kasashen da suka soke ta kan rufe Twitter.

Gwamnatin Najeriya ta gayyaci jakadun kasashen Amurka da Birtaniya da Kanada da Tarayyar Turai a kasar kan sukar ta da suka yi kan dakatar da kafar sada zumunta ta Twitter da ta yi.

A ranar Litinin wani jami’i a sashen sa ido da yada labarai a Ma’aikatar Harkokin Wajen Najeriya, Kimiebi Ebienfa, ya sanar da gayyatar jakadun zuwa wata ganawa da Ministan Ma’aikatar, Geoffrey Onyeama.

“Bayan dakatar da Twitter da Gwamnatin Tarayya ta yi da kuma raddin wadansu jakadu a kai, Ministan Harkokin Wajen Najeriya, Geoffrey Onyeama, yana kiran wadannan jakadun zuwa wata ganawa a yau (Litinin); Don haka muna gayyatar ku,” a cewar sanarwar.

Jakadun kasashen Yamma a Najeriya, sun soki lamirin gwamnatin kasar kan dakatar da Twitter tare da haramta amfani da shi a kasar.

Kasashen sun soki matakin na gwamnatin Najeriya da cewa yin karan tsaye ne ga ’yancin ’yan kasar na fadar albarkacin bakinsu.

Gwamntin ta dauki matakin ne kwana guda bayan Twitter ya goge sakon Shugaba Buhari a shafinsa na kafar, wanda a ciki ya gargadi masu tada kayar baya a yankin Kudu maso Gabas na kasar da sunan neman kafa kasar Biafra.