✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Dakatar da Twitter: Za mu hukunta wadanda suka karya doka — Malami

Twitter ya daina aiki a Najeriya bayan da Gwamnatin kasar ta dakatar da shafin a ranar Juma’a.

Atoni-Janar kuma Ministan Shari’a a Najeriya, Abubakar Malami, ya bayar da umarnin a gaggauta tuhumar duk wadanda aka samu da take dokar da Gwamnatin Tarayya ta bayar na dakatar da amfani da shafin Twitter a Kasar.

Wannan umarni na kunshe cikin wata sanarwar da Hadimin Ministan na Musamma kan Harkokin Sadarwa, Dokta Umar Gwandu ya fitar ranar Asabar a birnin Abuja.

Malami ya umarci Darektan Kula da Harkokin Shigar da Kara na Kasa (DPPF) da ke ofishinsa, da ya fara aiki tukuru wajen bin kadin wadanda suka karya wannan sabuwar doka ta hana amfani da shafin Twitter a Najeriya.

Ya umarci Darektan ya yi aikin hadin gwiwa tare da Ma’aikatar Sadarwar da Hukumar Kula da Harkokin Sadarwa NCC da sauran Hukumomi masu ruwa da tsaki domin tabbatar da hukunci kan duk wanda aka samu da laifin ba tare da bata lokaci ba.

Tuni dai shafin Twitter ya daina aiki a Najeriya bayan da Gwamnatin kasar ta dakatar da shafin a ranar Juma’a.