✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

‘Dakon kwantena daga China zuwa Legas ya fi daga Legas zuwa Kano arha’

Ya nemi ’yan kasuwa masu zaman kansu da su zuba jari a fannin jiragen kasa.

Hamshakin dan kasuwar nan na Najeriya, Abdussamad Isiyaka Rabi’u, ya shaida wa masu zuba jari cewa jigilar kwantena daga China zuwa Legas ya fi yin dakonta daga Legas zuwa Kano rahusa.

Abdussamad wanda shi ne mai Kamfanin BUA, ya bayyana hakan ne a birnin Paris na Kasar Faransa yayin da yake tsokaci kan irin kofofi na harkokin kasuwanci da ake da su a Najeriya musamman a bangaren harkar sufurin jiragen kasa.

A cewarsa, zuba hannun jari wajen kawo sauye-sauye a harkokin sufuri da dakon kayayyaki musamman a bangaren sufurin jiragen kasa, zai bude karin kofofin harkokin kasuwanci a kan wadanda ake da su a Najeriya, lamarin da ya ce zai janyo hankalin masu sanya jari.

Ya yaba wa gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari dangane da hobbasan da take yi wajen zuba jari a fannin sufurin jiragen kasa a fadin kasar nan.

A kan haka ne ya yi kira ga ’yan kasuwa masu zaman kansu da su zuba jari a fannin sufurin jiragen kasa.

Kazalika, Abdussamad ya ce Najeriya tana da albarkar kasar noma mai girman gaske, wanda hakan a cewarsa wata dama ce ta bunkasa harkokin kasuwanci da sarrafa ma’adanai da albarkatun kasa.