✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Daliba ta bude shafin koyar da Lissafi da harshen Hausa

Ta kirkiro manhajar koyon Lissafi kuma a shafinta akwai bidiyo iri-iri da ke koya darussan Lissafi daki-daki.

Wata daliba mai shekara 24, Fatima Ibrahim Madori, ta bude shafin koyar da darasin Lissafi ta hayar amfani da harshen Hausa.

Fatima, wadda ta kammala digirinta na farko fannin Kimiyyar Kwamfuta a Jami’ar Yusuf Maitama Sule da ke Kano ta ce ita da abokan aikinta biyu ne suka kafa shafin domin sauya yadda al’umma ke ganin Lissafi a matsayin darasi mai matukar wahala.

“Mun bude shafin domin saukake yadda ake koyarwa da kuma koyon darasin Lissafi ga daliban makarantun sakandare a Najeriya,” inji Fatima.

Ta ce babban abin da ya sa ake ganin wahalar darasin shi ne bambancin harshen da ake koyar da shi.

Hakan ne ya sa suko bude shafin da zai rika amfani da harshen Hausa wajen koyar da darasin domin kawar da matsalar

Ta ce a cikin shafin akwai bidiyo iri-iri na misalan darusassan lissafi da yadda ake bin su daki-daki.

Dalibar ta bayyana kwarin gwiwa cewa ganin gudummawar da suka samu daga hukumomi, shafin zai taimaka wajen saukake fahimtar darasin ga dalibai masu jin harshen Hausa.

“Na lura yawanci idan aka kammala darasin lissafi a aji dalibai kan bukaci a yi musu karin bayani da Hausa, abin da ya sa na gane cewa bambancin harshe ne ya sa ake ganin wahalar darasin.

“Shi ya sa da na samu dama, sai na kirkiro manhajar koyar da dalibai darasin da Hausa a intanet, daidai da manhajar koyarwa,” inji ta.

Fatima kara da cewa a halin yanzu tana kan aikin kirkiro da manhajar waya domin koyon darasin da Hausa, wanda dalibai za su iya saukewa su yi amfani da shi.

“Gaskiya ba karamin aiki ba ne saboda yana bukatar fassara wasu kalmomin Ingilishi zuwa Hausa, amma wasu kalmomin ban fassara su ba, saboda ba su da fassara a Hausa,” a cewar dalibar.

Ta ce ta shafe kusan wata uku tana aikin bude shafin, wanda nan gaba kadan za a kaddamar da shi a hukumance.

Fatima ta ce babban burinta shi ne ta taimaka wajen saukake koyo da koyar da darussan kimiyya, lura da yadda duniya ke sauyawa, kuma akwai bukatar Najeriya ta shiga a dama da ita a wannan fannin.