✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An yi garkuwa da dalibai 73 a Zamfara —’Yan sanda

An sace daliban bayan gwamantin jihar ta sanya sabbin matakan tsaro.

’Yan sanda sun tabbatar cewa dalibai 73 ne ’yan bindiga suka yi garkuwa da su a Makarantar Sakandaren Gwamnati da ke garin Kaya a Jihar Zamfara.

Tun da farko Aminiya ta kawo rahoton yadda ’yan bindiga suka kutsa makarantar da ke Karamar Hukumar Maradun ta Jihar, suna barin wuta a yayin da dalibai ke rubuta jarabawa, suka yi awon gaba da wasu dalibai a safiyar ranar Laraba.

Sanarwar da kakakin ’yan sandan Jihar Zamfara, Mohammed Shehu, ya fitar ta ce “Rundunar ’Yan Sandan Jihar Zamfara ta tabbatar cewa dalibai 73 ne aka yi garkuwa da su a Makantar Sakandaren Gwamanti da ke Kaya na Karamar Hukumar Maradun.

“An yi garkuwa da daliban ne bayan dandazon ’yan bindiga sun mamaye makarantar da misalin karfe 11:22 na safe.

“Rundunar, karkashin jagorancin Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar Zamfara, Ayuba N Elkanah, ta tura jami’ianta su bi sawun maharan, su gano su kuma ceto daliban da hadin gwiwar sojoji.

“An kuma tsaurara matakan tsaro a kauyen Kaya da makwabtansa da zummar dakile yiwuwar kai musu hari.

“Za kuma a sanar da mutane sauran matakan da aka dauka,” inji shi.

An sace daliban ne bayan Gwamnan Jihar Zamfara, Muhammad Bello Matawalle ya ba da umarnin rufe wasu kasuwanni da hanhoyi a sassan jihar.

Gwamnan ya kuma takaita adadin man fetur din da gidajen mai za su sayar wa masu ababen hawa, baya ga dokar hana fita daga almuru zuwa wayewar a Jihar.

A halin yanzu dai, Zamfara wasu jihohin yankin Arewa maso Yammaci da Arewa ta Tsakiya a Najeriya na fama da matsalar tsaro inda ’yan bindiga ke garkuwa da mutane domin karbar kudin fansa.

A karshen mako ne ’yan bindiga suka sako dalibai 90 da aka yi garkuwa da su a garin Tegina na Jihar Neja, domin karbar kudin fansa.

Kazalika an sako wasu daliban kwaleji a Jihar Zamfara da wasu ’yan kamarantar sakandaren Bethel da aka yi garkuwa da su a Jihar Kaduna.