✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Daliban Afaka 27 da aka sako sun isa Hedikwatar ’Yan sanda a Kaduna

Mafi akasarin daliban sun galabaita yayin da wasunsu rabin tsiraicinsu yake a bayyane.

Ragowar dalibai 27 na Kwalejin Horar da Harkokin Noma da Gandun Daji ta Gwammnatin Tarayya da ke Kaduna da aka sako sun isa ofishin ’yan sandan Jihar da yammacin Laraba.

Daliban da jami’an tsaro suka yi wa rakiya sun iso ofishin ne da misalin karfe 6.30 cikin wasu motoci bas biyu duk jikinsu ya yi yaushi tamkar marasa lafiya.

Wakilinmu ya ruwaito cewa, akwai alamun galabaita a tattare da daliban inda galibinsu ke tafiya da kyar da har wasunsu rabin tsiraicinsu a waje sakamakon kayan jikinsu da suke a yage.

A watan Maris ne ’yan bindiga suka afka kwalejin gandun dajin da ke Unguwar Mandoe a Kaduna suka saci dalibai 39.

Bayan iyaye da hukumar makarantar sun biya kudin fansa, an sako 10 daga cikinsu.

Daliban sun shafe kimanin watanni biyu a hannun ’yan bindigar gabanin sako su.

Wani daga cikin wadanda suka karbi daliban ya shaida wa Aminiya a yammacin Laraba cewa, fitaccen malamin Islama, Sheikh Ahmad Abubakar Gumi ne  ya sa baki aka sako su.

Aminiya ta ruwaito cewa, Gwamnan Kaduna Nasir El-Rufai, ya sha nanata cewa ba zai yi sulhu da ’yan bindiga ko ya biya kudin fansa ba.

Sakin daliban na zuwa ne bayan da Iyayensu suka gudanar da zanga-zanga a harabar ginin Majalisar Tarayya da ke Abuja a ranar Talata.