✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Daliban firamaren Kaduna sun tsere daga hannun ’yan bindiga

Daliban sun kubuta bayan masu garkuwar sun lakada musu duka

Dalibai uku daga cikin wanda aka yi garkuwa da su a makarantar Firamaren LEA Rama a Karamar Hukumar Birnin Gwari, Jihar Kaduna, sun tsere daga hannun masu garkuwa da su.

Daya daga cikin malaman makarantar ya shaida wa Aminiya cewar daliban sun tsere ne yayin da ’yan bindigar suka tsaya don satar shanu a wani kauye.

Wata malama da ta tsallake rijiya da baya makarantar, Naomi Francis, ta ta bbatar wa da Aminiya daliban uku sun kubuta, amma sun sha duka a hannun ’yan bindigar kafin su samu nasarar tserewa.

Sai dai kuma babu labari game da malaman da aka yi garkuwa da su tare da daliban.

Yadda aka yi garku da ’yan makarantar firamare

Da take bayyana yadda lamarin ya faru, “Sun zagaye makarantar ne bayan mun kammala taron da ake yi ko yaushe.

“Na fito aji sai na hangi daliban aji 5 da 6 na gudu, nan take na yi wa daliban ajina alama, su ma su tsere.

Wani mazaunin yankin, Mai Saje Rama shi ma ya tabbatar da dawowar daliban.

“’Yan bangar da suka bi sahu ba su yi nasarar gano inda suka shiga ba,” inji shi.

Da farko dai kansilan yankin Rama Aliyu Isa, ya musanta cewar ’yan bindiga sun tafi da dalibai.

Amma daga bisani Kwamishina Tsaro da Harkokin Cikin Gida na Jihar Kaduna, Samuel Aruwan ya tabbatar cewa an sace daliban.

Aruwan, ya sanar da cewar gwamnatin jihar za ta fitar da jawabi kan satar yaran.

Aminiya ta rawaito yadda satar daliban ta faru sa’o’i 24 bayan da jami’an tsaro suka dakile wani yunkuri na sace wasu daliba 307 na Makarantar Sakandiren Gwamnati da ke Karamar Hukumar Ikara da ke Jihar ta Kaduna.

Kazalika, jami’an tsaro sun dakile wani harin da aka kai rukunin gidajen ma’aikatan Hukumar Kula da Filayen Jiragen Sama da ke karamar hukumar Igabi a Jihar.

A daren ranar Alhamis, wasu ’yan bindiga sun fasa Kwalejin Gandun Daji ta Tarayya, da ke Afaka a Karamar Hukumar Igabi inda suka yi garkuwa da dalibai 39, wanda suka hada da mata 23 da maza 16.

Jami’an tsaro sun ceto dalibai 180, amma ’yan bindigar sun tsere da 39 daga cikin daliban, inda suka bukaci a basu N500 a matsayin kudin fansa.