✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Daliban Islamiyya 20 sun rasu a hatsarin kwalekwale a Kano

Daliban sun rasu ne a hanyarsu ta zuwa taron Mauludi a garin Bagwai da ke Jihar Kano

Wasu daliban Islamiyya sun rasu a sakamakon wani hatsarin kwalekwale a Karamar Hukumar Bagwai ta Jihar Kano.

Akalla dalibai 20 ne ake fargabar sun rasu bayan kifewar kwalekwalen a kan hanyarsu ta zuwa wani taron Mauludi ranar Talata.

“Yanzu da muke magana, ana ci gaba da aikin ceto, kuma jami’anmu sun gano gawarwaki 20 an kuma yi nasarar ceto wasu mutum bakwai da ransu,” inji kakakin Hukumar Agajin Gaggawa ta Jihar Kano, Saminu Abdullahi da misalin karfe 9.15 na dare ranar Talata.

Malam Saminu ya bayyana cewa gawarwaki 20 da aka gano na daliban Islamiyyar ne, kuma mutum 47 ne a cikin kwalekwalen a lokacin da abin ya auku.

Majiyarmu a Babban Asibitin Bagwai ta ce an kai gawarwaki 20 asibitin bayan kifewar kwalekwalen da ke dauke da mutum sama da 40.

Ta ce kwalekwalen ya yi hatsari ne da misalin karfe 4.30 na yamma a yayin da yake dauke da daliban makarantar Madinatu Islamiyya da ke kauyen Badau tare da sauran fasinjojin a kan hanyarsu ta zuwa garin Bagwai.

Ta kara da cewa mutanen da hatsarin kwalekwalen ya ritsa da su suna kan hanyarsu ce ta zuwa halartar taron Mauludi da reshen makarantar da ke garin Bagwai ya shirya.