✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Daliban Jami’ar Jos 2 sun mutu a rikicin matsafa

Rahotannin sun ce lamarin ya faru ne da misalin karfe 10 na daren ranar Litinin, a daidai lokacin da daliban suke dakunansu.

Akalla daliban Jami’ar Jos biyu ne aka hallaka sakamakon wani rikici da ya barke tsakanin wasu kungiyoyin matsafa a dakin kwanan dalibai na White House dake jami’ar.

Dakin kwanan daliban dai wanda yake a wajen makarantar na dab da unguwar ’yan majalisu dake kan hanyar zuwa Bauchi a garin Jos na jihar Filato.

Daliban dai wadanda lamarin ya shafa sun hada da Jakob Kefers, dan aji daya a Sashen Shugabanci da Tsare-tsare na Jami’ar da kuma Gideon Chongtami, wanda shi tuni ma ya kammala karatunsa daga Sashen Koyar da Wasan Kwaikwayo shima a Jami’ar.

Rahotannin sun ce lamarin ya faru ne da misalin karfe 10 na daren ranar Litinin, a daidai lokacin da daliban suke dakunansu.

Wani dan kato-da-gora a yankin ya shaidawa Aminiya cewa lamarin ya faru ne lokacin da wasu ’yan kungiyar matsafan da ba sa ga-maciji da juna suka kai harin ramuwar gayya a kan wasu abokan hamayyrasu dake zaune a dakin kwanan daliban.

Ya kara da cewa tuni ’yan sanda suka kai gawar daya daga cikin daliban zuwa Asibitin Koyarwa na Jami’ar Jos (JUTH), yayin da dayan kuma aka ajiye shi Asibitin Koyarwa na Bingham shima a Jos din.

Da muka tuntubi kakakin Rundunar ’Yan Sanda na Jihar Filato, Ubah Gabriel, ya yi alkawarin zai tuntube mu daga bisani.

Sai dai har zuwa lokacin hada wannan rahoton bai tunutba ba.