✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Daliban Kaduna: Har yanzu iyayen daliban ba su gana da su ba

Iyayen daliban sun koka kan rashin ba su damar ganawa da daliban da suka kubuta

Kwana daya da ceto wasu dalibai biyar na Kwalejin Gandun Daji da ke Afaka, Jihar Kaduna, har yanzu iyayensu sun ce ba su yi tozali da su ba.

Aminiya ta rawaito a ranar Litinin cewar sojoji sun kubutar da dalibai biyar daga cikin 39 da aka yi garkuwa da su a ranar 11 ga watan Maris, 2021 daga kwalejin.

Daya daga iyayen daliban, Friday Sanni, ya ce “Ba mu san su wa aka saki daga cikin daliban ba, mun je don mu gana da su an ce mana sai an kammala bincike sannan za a ba mu damar ganawa da su”.

Sai dai Gwamnatin Jihar Kaduna ba ta bayyana yadda aka kubutar daliban ba, amma ta ce an kai su sansanin soji, inda ake kula da lafiyarsu.

Dalibai biyar din da aka kubutar sun shafe tsawon kwana 25 a hannun wanda suka yi garkuwa da su, kafin su samu nasarar shakar iskar ’yanci.