✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Daliban KASU sun lakada wa sojoji duka a kan budurwa

Karbar lambar wayar daliba ya ja an yi wa hafsoshin sojin dukan kawo wuka.

Jami’ar Jihar Kaduna (KASU) ta tabbatar cewa wasu dalibanta sun lakada wa  wasu kananan hafsoshin soji da ke karatu a Jami’ar Soji ta NDA duka a kan wata budurwa.

Kura ta turnike tsakanin kananan sojojin da daliban ne a wurin bikin rantsar da sabbin daliban jami’ar da sojoin suka halarta ranar 12 ga watan Oktoba, 2021.

Da yake tabbatar da hakan a ranar Laraba, kakakin jami’ar KASU, Adamu Bargo, ya ce daliban sun kuma lalata motar sojojin, amma ya bayyana cewa an da dakatar da daliban da suka yi fada da sojojin.

“Lamarin ya faru ne a wajen bikin rantsar da sabbin dalibai, inda daya daga cikin kananan hafsoshin sojin ya yi kokarin karbar lambar wata daliba, amma ta ki.

“Wani dalibi ya shiga domin ya sulhunta lamarin, amma sai wani daga cikin sojojin ya tsinke shi da mari.

“Hakan ya sa sauran daliban da ke wurin suka yi wa sojojin taron dangi suka yi musu rubdugu da duwatsu da sanduna.

“Sojojin sun yi kokarin tserewa a cikin wata motarsu kirar Toyota Matrix, amma dalibai suka rufe kofar shiga jami’ar, sannan suka yi wa motar kaca-kaca.

“Daya daga cikin sojojin da bai samu ya shige cikin motar ba kuma dalibai sun ritsa shi, sun yi masa bugun tsiya,” a cewar Bargo.

Ya kara da cewar an fara gudanar da bincike kan lamarin, sannan za a dauki mataki kan daliban.

“Hukumar makaranta ba za ta lamunci duk wani nau’i na rashin da’a a wajen da ake koyon tarbiyya da halaye na gari ba,” kamar yadda ya bayyana.