Dalibi ya bindige abokinsa a cikin aji | Aminiya

Dalibi ya bindige abokinsa a cikin aji

    Abubakar Muhammad Usman

Wani dalibi mai shekara 16 ya harbe dan ajinsu  sannan ya harbe kansa, bayan wata rigima da ta faru tsakaninsu.

Hukumomin kasar sun ce lamarin ya faru ne a ranar Laraba, yayin da daliban ke shirin kammala zangon karatu don yin hutu a kasar Afirka ta Kudu.

Jami’an tsaro a kasar sun bayyana cewa dalibin ya dauko bindigar mahaifinsa ne ba tare sa sanin mahafin ba, ya kuma shiga da ita makarantar ba tare sa kowa ya sani ba.

Ana tsaka da karatu a cikin aji ne dalibin ya fito da ita ya harbi dan ajin nasu da suka samu sabani a kirji, nan take ya mutu ba tare da ya shura ba.

Daliban ’yan aji daya ne na babban sakandare a Makarantar Sakandaren Lesiba da ke Daveyton.

Tuni jami’an tsaro suka shiga gudanar da bincike don gano abin da ya hadda lamarin.

Kazalika, an ba da umarnin yi wa gawar dalibin da ya yi kisan tare da kashe kansa gwajin kwakwalwa.