✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Dalibi ya soka wa abokin karatunsa wuka a Bauchi

Suna takar dambe wanda ake zargin ya ciro wuka daga aljihunsa ya soka masa a ciki.

Wani matashi mai shekaru 22 da ke ajin karshe a Kwalejin Ilimi ta Adamu Tafawa Balewa ya soka wa wani abokin karatunsa mai suna Usman Umar wuka.

Kakakin rundunar ‘yan sandan Jihar Bauchi, SP Ahmed Wakil ne ya bayyana hakan ga manema labarai ranar Laraba, inda ya ce tuni wanda ake zargin ya shiga hannu.

“A ranar 28-11-2022 ne da karfe 1:00 na rana muka samu labarin wani dalibi da ke ajin karshe a Kwalejin Ilimi ta Tafawa Balewa ya soki abokin karatunsa mai suna Usman Umar mai shekaru 25 da wuka a ciki.

“Lokacin da ‘yan sandan sashin bincike suka isa wurin da lamarin ya faru, sun dau Umar zuwa asibiti, inda likitoci suka tabbatar da ya riga mu gidan gaskiya.

“Daga nan ne muka fara binciken musabbabin rigimar, inda muka gano wanda ake zargin da margayin abokai ne da ke shekarar karshe a Kwalejin.”

“Rigima ta barke tsakaninsu ne bayan margayin ya tuhumi wanda ake zargi da tafiya wani wuri ba tare da ya sanar da shi ba.

“Daga nan dambe ya kaure tsakaninsu sai wanda ake zargin ya ciro wuka daga aljihunsa ya soka masa a ciki.

“Mutum biyu sun ba da shaidar lamarin ya faru a kan idonsu, kuma dukkansu daliban makarantar ne.

Wakili ya kuma ce yanzu haka suna ci gaba da bincike, kafin mika wanda ake zargin kotu.