✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Dalibin jami’a ya kashe kishiyar mahaifiyarsa da tabarya, ya karya mahaifinsa

Ya kua karya kafar mahaifinsa da tabaryar

Wani matashi dalibin jami’ar Tarayya da ke Dutsin-Ma a jihar Katsina, Najib Shehu, ya kashe kishiyar mahaifiyar ta hanyar buga mata tabarya a ka, har sai da ta ce ga garinku nan.

Kazalika, matashin mai kimanin shekara 25, ya kuma karyar kafar mahaifinsa da tabaryar lokacin da ya fito daga dakinsa a lokacin da yake jin ihun matar tashi, don ya kai mata dauki.

Lamarin dai ya jefa mazauna unguwar Ambasada da ke birnin Katsina, inda ya faru, cikin fargaba.

Najib dai na matakin aji uku a karatunsa a jami’ar.

Majiyarmu ta shaida mana cewa tun a baya Najib ya sha shan alwashin cewar sai ya kashe matar mai suna Asiya Muhammad saboda yadda ya ce tana takura masa a gidan.

Sai dai majiyar, wacce ta nemi a sakaya sunanta ba ta tabbatar da ko mahaifiyar shi Najib din tana gidan ko tana tare da mahaifin ba ko kuma a’a.

Kazalika, an ce bayan ya biyo kanwar shi da tabaryar a guje zuwa kofar gida inda ya tsaya yana cewa duk wanda ya matso kusa da shi zai kashe shi.

Amma a nan ne a cewar majiyar jama’ar unguwar suka yi tara-tara suka kama shi sannan suka mika wa ’yan sanda.

Kakakin ’yan sandan jihar ta Katsina, SP Gambo Isa, ya tabbatar da faruwar lamarin yayin da yake gabatar da Najib ga manema labarai.

Ya ce da zarar sun kammala bincike a kai za su gurfanar da shi a gaban kuliya.