✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Dalibin likitancin da ke sana’ar abinci saboda yajin aikin ASUU ya rasu

Dalibin nan da ya kama sana’ar sayar da abinci a sakamakon yajin ASUU, Usman Abubakar-Rimi, ya kwanta dama. Kafin rasuwarsa, marigayin dalibi ne a ajin…

Dalibin nan da ya kama sana’ar sayar da abinci a sakamakon yajin ASUU, Usman Abubakar-Rimi, ya kwanta dama.

Kafin rasuwarsa, marigayin dalibi ne a ajin karshe a fannin likitanci a Jami’ar Usmanu Danfodiyo ta Sakkwato (UDUS).

Ya kama sana’ar sayar da abinci ne don maganin zaman kashe wando ganin cewa yajin aikin ASUU ya ki ce, ya ki cinyewa.

Abubakar-Rimi ya bude shagon cin abinci ne a birnin Sakkwato inda yake sarrafa rakiyar yara ga mabukata.

Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN) ya ce, Usman ya rasu ne a ranar Laraba bayan fama da takaitaccen rashin lafiya.

Amma sai a ranar Asabar aka tabbatar wa NAN batun rasuwar, kuma tuni aka yi jana’izar marigayin kamar yadda addinin Musulunci ya tanada a mahaifarsa, Rimi da ke Jihar Katsina.