✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Dalilai biyar da suka sa Messi neman barin Barcelona

Lionel Messi ya sanar da kungiyar kwallon kafa ta Barcelona aniyarsa na ficewa daga kungiyar a kakar wasa mai zuwa. Barca ta wa kamfanin dillancin…

Lionel Messi ya sanar da kungiyar kwallon kafa ta Barcelona aniyarsa na ficewa daga kungiyar a kakar wasa mai zuwa.

Barca ta wa kamfanin dillancin labarai na AFP ce gwarzon dan wasan ya sanar da ita a ranar Talata, ‘yan kwanaki bayan kungiyar ta nada Ronald Koeman a matsayin sabon mai horas da ‘yan wasanta.

Messi ya tunatar ta kungiyar yarjejeniyar da ke tsakacinsu cewa zai iya barin kungiyar ba tare da biyan £632m ba karshen kowace kakar wasanni.

Tun a watan Mayu da kwangilarsa ke karewa aka fara rade-radin tafiyar Messi amma lauyansa ya ce za a tsawaita saboda tsaikon da aka samu akamakon bullar annobar coonavirus.
Yanzu kintacen ya zama tarihi ‘yan kwanaki bayan an yi ta ta kare a kasar gasar cin kofin Zakarun Turai wanda aka buga a ranar Lahadi tsakanin PSG bayan Bayern Munich wanda shi ne karshen kakar ta bana.

Tuni dai aka fara hasashen idan har Messi mai shekara 33 ya bar Barca, to kungiyoyi irinsu PSG da Manchester City za su dauke shi.

Tun bayan bakar kunyar da ta sha a hannun kungiyar Bayern Munich a karawar da ta yi da ita a gasar Zakarun Turai, Barcelona na ci gaba da fuskantar tasgaro da ke shafar hukuncin kasancewar tauraron dan wasa Lionel Messi tare da kungiyar ko kuma ta raba gari da shi.

Bayern Munich ta yi wa Barcelona bugun fin karfi inda ta lallasa ta ci 8-2 a wasan kwata final na gasar Zakarun Turai da suka kara a filin wasa na Estadio da Luz da ke kasar Portugal.

Wannan mummunan rashin nasara ya haifar da tarzoma inda masoya kungiyar ke kiraye-kirayen sauya tsarin gudanarwa da kuma fasalin ‘yan wasa a kungiyar.

Husumar da ta kunno kai ta yi sanadiyar sallamar mai horas da ‘yan wasan kungiyar, Quique Setien, inda aka maye gurbinsa da wani tsohon dan wasa da ya taba taka leda a kungiyar, Ronald Koeman.

Sai dai a yanzu ido ya koma kan tauraron dan wasa na kungiyar, Lionel Messi, inda rahotanni a kasar Andalus ke ikirarin cewa ya fusata kuma akwai yiwuwar zai san inda dare ya yi masa a kakar wasanni mai zuwa.

Messi dai ya shafe gaba daya rayuwarsa ta kwallon kafa a kungiyar Barcelona kuma ya lashe kofuna bila adadin, inda har a wasu lokutan ya sha yin ikirarin cewa yana sha’awar karkare buga tamola a kungiyar har ya zuwa lokacin da rataye takalmansa.

Ga wasu jerin dalilai biyar da ka iya zama musabbabin sauya shekar Messi ya sauya sheka ta barin Barcelona:

  1. Gaza dawo da Neymar Kungiyar

Gazawar Barcelona wajen dawo da tsohon dan wasanta, Neymar ya fusata Messi kwarai da aniya.

A baya an rika yada jita-jitar cewa Barcelona tana zawarcin Neymar don dawo da shi cikinta daga kungiyar PSG, amma hakan bai tabbata ba.

Wannan lamari ya rushe kyakkyawan zato da Messi yake yi na dawowar abokinsa wanda sun kulla alaka ta fahimtar juna a kan sana’ar da suka rika.

  1. Sallamar Valverde

Akwai dangartaka mai karfi tsakanin Messi da tsohon mai horas da ’yan wasa na kungiyar Barcelona, Enersto Valverde. Sai dai hakan bai sa kungiyar ta fasa sallamar sa ba sakamakon rashin kokarin da ya yi.

Wannan hukunci bai yi wa Messi dadi ba sakamakon kyautata wa Valverde zato da yake yi na ganin cewa zai iya kawo maganarcin sauyi a kungiyar duk da korafin da magoya baya ke yi.

  1. Caccakar ’yan wasan Barcelona da Abidal ya yi bayan sallamar Valverde

Sallamar Valverde ta sanya Daraktan Harkokin Wasannin Barcelona, Eric Abidal caccakar ’yan wasan kungiyar da cewa rashin kokarinsu da kuma rashin ba da hadin kai ne ya janyo haka.

Hakan ya sanya Messi ya marya wa da Abidal raddi da cewa, ya yi abin da ya shafe shi kuma duk wani hukunci da aka zartar a kungiyar da amincewarsu.

  1. Rashin fahimtar juna tsakanin Messi da Setien

Ba a samu kyakkyawar alaka da fahimtar juna ba tsakanin Messi da Setien sabanin yadda ta kasance tsakaninsa da Valverde.

Rashin wannan jituwa da ke tsakaninsa da Messi ta sanya zaman Setien a kungiyar ya zamto marar dadi.

  1. Mummunan tasirin da annobar coronavirus ta haifar

Durkushewar  tattalin arziki da annobar coronavirus ta haddasa wanda sanadiyarsa aka rage albashin ’yan wasan Barca da kashi 70 cikin 100 bai yi wa Messi dadi ba.

Messi ya nuna bacin ransa matuka dangane da yadda har kungiyar ta bari wannan lamarin ya shafi ’yan wasa ba tare da tsinana wani abu ba kafin ta yanke shawarar hakan.