✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Dalilan Da Buhari Zai Yi Kidayar Jama’a a yanayin rashin tsaro

Dalilin da matsalar tsaro ba za ta hana gudanar da kidayar jama'a ba.

A kwanan Mannir Dan-Ali ya tattauana da Babban Hadimin Shugaban Kasa Muhammadu Buhari, Malam Garba Shehu, a tashar Trust TV, inda ya yi karin haske kan harin da aka kai wa jirgin kasan Abuja zuwa Kaduna da batun shirin kidayar al’umma da ke tafe da kuma afuwar da Shugaba Buhari ya yi wa tsoffin gwamnoni, Joshua Dariye na Filato da takwaransa Jolly na Taraba. Ga dai yadda hirar ta kasance:

’Yan kwanakin da suka shude Majalisar Zartarwa ta ba da sanarwa za a gudanar da kidayar al’ummar kasa a watan Afrilu, shin mene ne dalilin da kuka ga dacewar gudanar da kidayar duk da sukar da ta sha?

Da farko, bisa tsarin Majalisar Dinkin Duniya, akan gudanar da kidaya ne duk bayan shekaru 10, amma a namu bangaren tun kidayar da aka gudanar a 2006 ba a sake yin wani ba.

An bijiro da batun kidayar ga majalisa ne saboda abu ne da kundin tsarin mulki ya tanada cewa kafin gudanar da shi wajibi shugaban kasa ya sanar da majalisar.

Kafin wannan lokaci an yi yukurin haka, ba wai yanzu ne aka soma ba.

Hukumar Kidaya tana shirye-shirye da kuma aikin sanya wa gidaje alamomi a duk fadin kasa.

Sun riga sun fitar da duka taswirar da ake bukata, abun da ya rage shi ne gwamnati ta ba da izinin ci gaba da aiki.

Suna lura da abin da ke gudana ne a kasa, misali, ya kamata a ce an gudanar da shirin na gwaji a watan Mayu amma duba da yadda ’yan siyasa suka maida hankali wajen kokarin gudanar da zabubbukan fidda gwani hakan ba zai samu ba.

Wannan ya sa aka jinkirta zuwa bayan kammala zabubbukan fidda gwani na jam’iyyu.

Sai dai damuwar jama’a ita ce yadda a kasa ake fama da matsalar tsaro, wadda ta raba mutane da dama da mazaunansu wanda hakan ya sa wasu ke tunanin ta yaya za a iy a kidaya jama’a a cikin irin wannan hali alhali kamata ya yi shirin kidayar ya cim ma jama’a a mazauninsu?

Duk da dai suna da damar fadar ra’ayinsu, amma abin ya ba ni mamaki, cewa tun da gwamnati na fuskantar matsaloli a wasu yankuna don haka ta dakatar da shirin har ma a yankunan da ba su fuskantar wata matsala.

Dole ne gwamnati ta ci gaba da shirinta.

Kana nufin har kauyukan yankin Arewa maso-yamma, duk da cewa a baya-bayan nan an ji Shugaban Majalisar Dokokin Jihar Borno na cewa har yanzu karamar hukumarsu da wasu wurare na karkashin Boko Haram?

Bari mu dauki wannan daya bayan daya.

na yi ammanar cewa Gwamnan Jihar Borno, Zulum, ba mayaudari ba ne; kwana uku da suka gabata ya shaida wa majalisa cewa kusan duk manyan hanyoyin da ke fadin jihar an sake bude su, haka ma manyan kasuwanni da hada-hadar kan iyaka.

Ita ma karamar hukuma daya tilon da ta rage karkashin kulawar sojoji ita ma mazaunta sun koma gidajensu.

Idan kuwa kana da wata tambaya da ta danganci daidaita zancen shugaban majalisar da na Gwamna Zulum, ina ganin zai fi dacewa ka yi musu ita.

Amma bayanan da gwamnati take samu su ne, an ci karfin matsalar tsaro a yankin Arewa.

Sannan cigaban da aka samu a fannin tsaron na tabbatar wa ’yan kasa cewa an karya lagon Boko Haram.

Ba wai ana nufin ba za su iya kai hari a kowane lokaci ba ne, amma kuma jami’an tsaro na farautar su.

Kalli abin da Kididdigar Ta’addanci ta Duniya ta nuna game da sha’anin tsaron Najeriya, yabawa ta yi wa gwamnati kan yadda ta samu nasarar kawar da kashi 90 cikin 100 na ayyukan Boko Haram, don haka ana samun cigaba.

Duk da dai kafafen yada labarai na zamani ba su maida hankali wajen yada nasarar da aka samu ba wannan wani abu ne daban, amma gaskiyar ita ce yankin Arewa maso Gabas na karkashin kulawar da ta dace.

Wasu ma cewa suke yi hatta jiragen yaki na Super Tucano da aka sayo kimanin shekara guda yanzu babu wani amfani da suka yi wajen yaki da ta’addanci; sai muka fara ji ana cewa an kasa amfani da jiragen ne saboda wai akwai wasu sharudda da aka gindaya a kansu.

Idan kana mu’amala da kasashe irin Amurka dole ka zama mai taka tsan-tsan da ra’ayoyin jama’a wanda abu ne mai muhimmanci a gare su da mu kanmu.

Gaskiya ne lokacin da suka sayar wa gwamnatin Najeriya jiragen Super Tucano sun yi la’akari da dokar kasarsu.

Dokar tasu ba ta yarda a yi  amfani da makamai a kan farar hula ba, in kuwa ba haka ba Amurka ba za ta sayar muku da makaman ba.

Kada ka manta cewa an dauki shekaru ana neman sayen makaman amma Amurka ta ki amincewa sai a zuwan Buhari ne aka cim ma nasarar hakan.

Gaskiya ne cewa da farko, sojojin sama ba su yi amfani da jiragen ba wajen yaki da matsalar tsaro a Arewa maso Yamma.

Bayan haka ma an dade kafin a fara amfani da su saboda abubuwa ne masu amfani da makamai na musamman.

A fahimtata abu ne da ba zai samu ba har sai zuwa watan Maris zuwa shiga Afrilu.

Alhamdulillahi, kasancewar gwamnati ta maida hankali matuka wajen amfani da fasahar zamani a sha’anin yaki da ta’addanci, an samu nasarori da daman gaske a Arewa maso Yamma.

Me za ka ce wa iyalan wadanda aka yi garkuwa da su a harin jirgin kasan Abuja zuwa Kaduna, wadanda suka shiga kafafen yada labarai don mika kukansu ga Shugaban Kasa ya taimaka a dawo musu da ’yan uwansu.

Ina mai tsausayawa dangane da halin da suke ciki na damuwa; sannan shi kansa Shugaban Kasa ya damu da lamarin.

Amma su kara hakuri, saboda sojoji da ’yan sanda da sauran hukumomin tsaro suke gudanar da harkokinsu.

Magana muke a kan a yi amma a shafe ba. Idan da a ce bukatar shafewa ake da ita, ana iya kammala komai cikin sa’o’i 24.

Ko dai wannan ne ya sanya har yanzu ake rike da ’yan matan Yauri?

Na fada maka cewa su sojoji da yadda suke gudanar da aikinsu.

Aikin ya rataya ne a kan Shugaban Kasa, muna son ya koma Kaduna ko Daura da zama ya huta bayan kammala mulkinsa.

Ba mu so mu ji an maka shi a Kotun Manyan Laifuka ta Duniya. Mu kyale sojoji su yi amfani da horon da suka samu wajen yaki da wadannan matsaloli.

Me ya sa babu wani hukunci da aka a yi kan ma’aikatan da ke kula da layin dogon duk da an shawarce su da su dakatar da jirgin tattare da cewa Manajin Darakta ya tabbatar da an yi hakan; amma duk da haka shi bai yi murabus ba kuma Ministan Sufuri bai tsige shi ba?

Kana da yadda kake kallon lamarin, su ma haka lamarin yake gare su.

A duk fadin duniya babu wata kasa da ke son a rika yi mata kallon ta mika kai ga ’ya ta’adda.

Idan kuwa kuka aikata haka, ba za a taba kawo karshen ta’addancin ba; ba za mu bari ’yan ta’adda su tsara wa kasa dokokinta ba.

Me kake gani zai faru idan ba mu da karfin kare ’yan kasa da rayukansu ke cikin hadari yayin da ’yan ta’adda suka himmatu wajen kai hare-hare kamar yadda ya faru a Kaduna?

Ka fahimce ni, babu wanda zai kare wata gazawa da aka yi.

Kai yi wa yi Amaechi wasu daga cikin wadannan tambayoyin nan gaba a cikin shirinku.

Amma ai maigidanka (Shugaban Kasa) mai iko ne kan ayyukan Ministan Sufuri, yana iya tsige shi amma ya ki, ko kuwa dai babu wanda alhakin gazawar ya rataya a kansa ne?

A bisa wasu dalilai ne zai tsige Amaechi?

Jami’an tsaro sun ba da shawara a kan tafiye-tafiyen.

Ku bi a hankali game da irin abubuwan da kuke karantawa a kafafen sadarwa na zamani, ka tabbatar da ka san gaskiya.

Ke nan kana nufin bayanan tsaron karya ne, cewa babu wani bayani da ya nuna yiwuwar aukuwar wadannan hare-haren sannan babu abin da aka yi a kai?

A’a, abin da nake cewa shi ne babu yadda za a yi Shugaban Kasar da nake yi wa aiki ya samu labarin cewa gobe za a kai hari kan kaza da kaza sannan ya ce kada a yi komai a kan haka.

Daya daga cikin kudurorin Gwamnatin Buhari shi ne yaki da rashawa, an yi ta ce-ce-ku-ce duk da cewa Malisar Tsofoffin Shugabannin Kasa ta yi afuwa ga wasu tsoffin gwamnoni biyu. Ba ka ganin hakan zai isar da wani sako mara kyau?

Lamarin na dauke da abubuwa guda biyu; na farko, ban son in yi magana a kan karfin da sashe na 175 na Kundin Tsarin Mulki ya bai wa Shugaban Kasa.

Shugaban Kasa na yana ikon da zai yi ahuwa ga dukkan laifuffukan da aka aikata ba tare da wasu sharudda ba.

Duk da haka akwai ka’idojin aiwatar da wadannan abubuwa, daga ciki akwai rashin lafiya da stufa.

Majalisar Tsofoffin Shugabannin Kasa da ta mara wa Shugaba Buhari awaitar da hakan dattawan kasa ne.

Wannan ya sa a lokacin da suke tattaunawa wancan dattijon da aka yanke wa hukunci zaman gidan kaso na tsawon shekaru 120 aka sallame shi ya koma gida bayan wata shida,  a nan aka ce wannan ba daidai ba ne saboda wai hakan zai isar da mummunan sako, don haka ba wai mun bata hanya ba ne.

Abin shi ne cewa siyasa za ta shigo ciki — Haka yake faruwa a ko’ina.

Idan Shugan Amurka ya yi wa masu laifi afuwa, mutane za su fada mishi cewa ya yi haka ne saboda siyasa.

Yaya batun wadanda suka saci akuya amma shekara da shekaru suna tsare a kurkuku?

Saboda ’yan jarida sun mayar da hankalinsu a kan wadannan mutum biyu kasancewarsu jigogi ne a siyasa.

Amma da za a fitar da jerin sunaye 160, a ciki za ka tarar da wadanda ba a bakin komai suke ba wadanda ’yan jarida ba su damu da lamarinsu ba, shi ya sa ba a batunsu.

 Mataimakin Shugaban Kasa ya nuna kwadayinsa kan takarar shugaban kasa, ko yaya Shugaban Kasa ya kalli lamarin?

Ba na kusa lokacin da Shugaban Kasa ya gana da da shi kuma ba a yi mini wani bayani a kan haka ba.

Ko kana murnar ganin wanda shi ne ke biye da Shugaban Kasa ya zo ya ci gaba da ayyukan da kuka fara?  

Wannan kuma abu ne da ’yan jam’iyya za su yanke shawara.

Amma idan ana batun hadin kai APC ce kan gaba a Afirka.

Duk da cewa Shugaban Kasa na da ta cewa amma shugabannin jam’iyya ne za su yanke matsaya.