✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Dalilan da mata ke son miskilin namiji

Mata da yawa sun fi son maza masu dabi’ar ta miskilanci fiye da masu haba-haba.

Ana yawan ganin miskilai a matsayin mutane masu girman kai ko raini da wulakanci saboda shiru-shirunsu, sai dai kuma ba haka abin yake ba, dabi’arsu ce haka.

Sai dai kuma duk da haka, mata da yawa sun fi son maza masu wannan dabi’ar ta miskilanci fiye da mutum mai haba-haba.

Mujallar Tozali ta kawo dalilan da ke sa mace ta so miskilin namiji kamar haka:

  1. Suna da kokarin saurarar mutane saboda ba su damu da sha’anin mutane ba.
  2. Samun isasshen lokacin magana da mutane saboda ba su da yawan magana da mutane daban-daban
  3. Sun iya kwantar da hankalin yarinya saboda shirun yana basu damar  su lakanci halayyar mutane.
  4. Suna da saurin fahimtar zancen mutane saboda ba kowace magana suke maida hankali a kai ba.
  5. Ba su da saurin mita ko korafi saboda shiru-shirunsu.
  6. Ba su da nuna takama da alfahari da suke da shi saboda su ba su ga dalilin yin hakan ba.
  7. Sukan koya wa mace yadda za ta kula da kanta saboda lokacin da suke da shi na nazartar halayyarta.