✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Abin da ya sa tun tuni ya kamata Buhari ya kori hafsoshin tsaro

Kwararru a fannin tsaro sun ce tun tuni ya kamata Shugaba Muhammadu Buhari ya sallami hafsoshin tsaro a aikace, don haka lokaci ya wuce na…

Kwararru a fannin tsaro sun ce tun tuni ya kamata Shugaba Muhammadu Buhari ya sallami hafsoshin tsaro a aikace, don haka lokaci ya wuce na ya kara sa su wani aikin magance matsalar tsaro. 

Bayanan masanan da suka ce gazawar hafsoshin tsaron ta dade da gundurar ‘yan Najeriya, na zuwa ne bayan Shugaban a karon farko ya shaida wa hafsoshin tsaron cewa bai gamsu da abin da suke yi na magance matsalar tsaro ba kuma ba su da uzuri.

Kalaman nashi sun zo ne a sadda ake zanga-zanga da korafe-korafe sakamkon hare-haren ‘yan bindiga da suka addabi yankin Arewa-masa-Yamma, musamman jiharsa ta Katsina, inda suka kashe kusan mutun 100 a mako guda.

Masu zanga-zangar sun bukaci Buhari ya sauka daga mulki tare da gwamnan jihar Aminu Masari wanda ya ce ya yarda gwamnatinsa ta kasa kare rayuka da dukiyoyin jama’ar jihar.

Mai ba Shugaban Shawara kan Tsaro, Babagana Monguno yayin bayyana  yadda tattaunawar da shugaban kasa da hafsoshin tsaron ya kasance ya ce Buhari ya kuma umarce su da su yi aiki tare wajen shawo kan matsalar da ke gabansu.

Ya kamata Buhari ya tisa keyar hafsoshin tsaro, inji kwararru
Shugaba Buhari yayin ganawa da Manyan Hafsoshin Tsaron, suna sauraron bayani Babban Hafsan Rundunar Sama, Abubakar Sadique [wanda ba a nuna a hoton ba]. A dama da shi Babban Hafsan Tsaro Gabriel Olanisakin ne sanye da da riga mai doguwar hannu ya bude farin fayil. Sai Kwamdan Sojin Kasa, Tukur Buratai da irin rigarsa Olonisakin mai gajeren hannu, sai kuma Babban Hafsan Sojin Ruwa, Ibok Ete Ibas sanye da fararen kayan soji.
Buhari wanda ya ce wa hafsoshin dole su mike su yi aikinsu ko su san inda dare ya yi musu, ya kuma yi musu kashedi game da kara tabarbarewar matsalar.

Amma kwararru a fannin tsaro sun ce ba su gamsu da hakan ba, domin tuntuni ya kamata ya maye gurbinsu da sabbin jini a kuma sauya tsarin tsaron kasar domin kawo kashe-kashen ‘yan bindiga da sauran matsalolin tsaro a kasar.

Ba maganar fatar baki ba ce

Da yake sharhi kan umurnin Shugaban Kasar, masanin tsaro kuma mai nazari kan ayyukan ta’addanci, Dokta Amaechi Nwaokolo ya ce ya kamata Buhari ya yi a gani a aikace cewa bai gamsu da hafsoshin tsaron ba.

Dole Buhari ya kawo sabbi tun da ya dade yana ba wa hafsoshin tsaron na yanzu irin wannan umarni amma har yanzu ba ta sauya zane ba, inji shi.

“Mun gaji da wadannan ba da umarnin da babu samako. Ba a bukatar su tun da sun yi iya kokarinsu amma suka kasa.

“Shugaban Kasa ya bincika, ya yi sabon zubi. Akwai wasu da dama da suka fi wadannan iya kamun ludayin”, inji shi.

Abin da ya kamata Buhari ya yi yanzu

Salihu Buhari tsohon soja ne, wanda ya ce ya kawo yanzu ya kamata Shugaban Kasa ya yi aki da kiraye-kirayen jama’a cewa ya sallami hafsoshin tsaron, a fitar da sabon salon yaki sannan a samar wa sojojin isassun kayan aikin da suka dace.

A cewarsa hanya guda ta ba wa dakaru kwarin gwiwar yin aikinsu yadda ya kamata shi ne a wadata su da dukkan kayan aikin da suke bukata.

Ya yi bayanin cewa kayan aikin da aka sayo wa sojoji a 2014 ne suka ba su karfin fatattakar ‘yan Boko Haram daga kananan hukumomi 35 a jihohi uku na Arewa ta Gabas, suka rage a karamar hukuma daya tal kafin a sauya gwamnati a 2015.

An dade dana ruwa kasa na shanyewa

“Abu na biyu shi ne ya sauya hafsoshin tsaro domin sojoji sun riga sun debe kauna da shugabancinsu. Babu wani sabon abun da waninsu zai kawo da ba a yi ba a shekaru biyar din da suka gabata.

A cewarsa muddin ba a murkushe ‘yan ta’adda ba kafin damuna ta kankama, to karshenta sai dai a jira zuwa watan Disamba, lokacin da dazuwa suka bushe.

“Gargadin na iya kaiwa har zuwa 2023. Kawai ya ba su wa’adin magance matsalar kuma idan lokacin ya cika bukata ba ta biya ba, ya yi waje da su.

“Maganar su je suna yi wa shugaban kasa bayani har ya yarda cewa abubuwan da ke kawo ranshin tsaro su ne ta’ammuli da kwayoyi da makamai da ke hannun mutane da kuma layukan waya marasa rijista ba hujja ba ce.

“Yanayin da ake ciki ya wuce a zauna ana dora wa wata ma’aikata laifi. Tunda har aka shigo da sojoji ciki, ai ta tabbata cewa abin ya gagari dukkan sauran hukumomi.

“Kashe-kahen ya yi yawa, amma ya ki sauraran mutane. Tunda yanzu ya ga ana zanga-zanga, zai iya fadar abin da ya ce yanzu.

“Sau biyu yana kaddamar da aikin soji na musamman a Zamfara, yanzu ga wani ana yi a Katsina, wata biyu ken nan amma har yanzu babu inda haka ta cimma ruwa.

‘Muna gudun taba fararen hula ne’

A nasa bangaren Darektan Yada Labarai na Rundunar Tsaron, Manjo Janar John Enenche, ya ce babban cikas din da suke samu a yaki da ‘yan bindiga a Arewa ta Yamma shi ne guje wa taba fararen hula.

John Enenche a jawabinsa kan aikace-aikacen rundunar ya ce ‘yan bindiga sun fahimci dokokin kasa da kasa na hana taba fararen hula, shi ya sa suke shiga cikinsu su fake.

“Ba rauni gare mu ba. Sojoji na da karfin tarwatsa wuri cikin dan kankanin lokaci, amma matsalar ita ce fararen hula da ba su ji ba, ba su gani ba”, inji shi.

Wata matsalar kuma a cewarsa ita ce rashin samun muhimman bayanan sirri daga wurin jama’a.

Amma ya ce duk da haka sojoji na samun gagarumar nasara a yakin da suke yi  da ‘yan bindiga a yankin, sakamakon hare-haren da suke kaiwa a maboyarsu ‘yan bindigar da jiragen yaki da kuma ta kasa.

An ci gaba da zanga-zanga

Daruruwan mutane, wadanda yawancinsu daliban manyan makarantu ne daga wurare daban-daban sun yi wa garin Katsina, mahaifar Shugaba Buhari tsinke, suna neman wasu manyan jami’an gwamnatin jihar su sauka daga mukamansu.

‘Yan sanda sun yi wa masu zanga-zangar a kan tituna, suka kuma tsare su, bisa zargin tayar da fitina.