✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Dalilin da aka dakatar da shirin ‘Idon Mikiya’

Ana zargin gwamnati ta dakatar da shirin ne saboda kwance mata zani a kasuwa da ake yi galibi a cikin shirin.

A jiya Talata ce Gwamnatin Najeriya ta dakatar da watsa shahararren shirin nan mai suna Idon Mikiya wanda gidan rediyon Vision FM mai cibiya a Abuja ya saba gudanarwa.

Bayanai sun ce ana zargin gwamnatin ta dakatar da shirin ne saboda kwance mata zani a kasuwa da ake yi galibi a cikin shirin.

Sai dai a wata takarda mai dauke da umarnin dakatarwar wadda Hukumar Kula da Gidajen Rediyo da Talabijin ta Kasar (NBC), ta aika wa gidan rediyon ta ce ta dauki matakin ne sakamakon shirin da aka gudanar na kai tsaye a tashar ranar 5 ga watan Janairu 2022 da kuma tashar talabijin ta Farin Wata.

Sanarwar ta ce a shirin ranar wanda aka tattauna batutuwa ciki har da na nadin mukamai a Hukumar Bayanan Sirri ta Kasa (National Intelligence Agency, NIA), tashar ta saba wa tsarin mulki na Najeriya, sashe na 39(3)(b), wanda ya takaita magana a kan abubuwan da suka shafi hukumomin tsaro na gwamnati.

Hukumar ta ce a lokuta da dama ta gayyaci hukumar gidan rediyon na Vision FM a kan batutuwan da suka shafi aikin yada labarai, na tabbatar da adalci ga kowane bangare da ji daga kowane bangare da labari ya shafa da kuma kauce wa bayyana ra’ayin mai gabatar da shiri, wadanda dukkaninsu sun saba wa dokokin yada labarai.

A dangane da hakan ne hukumar ta dakatar da tashar daga watsa shirin tun daga ranar 28 ga watan Janairu 2022, tsawon wata shida, tare kuma da cin tarar hukumar rediyon naira miliyan biyar.

“Idon Mikiya” shiri ne mai farin jini wanda wasu fitattun manyan ’yan jaridu da mammalakan gidan rediyon Vision FM suke gabatarwa daga Abuja ciki har da Umar Faruk Musa da Shu’aibu Mungadi da kuma Abubakar Kabiru Matazu.

Ana watsa wannan shirin na “Idon Mikiya” a duk ranakun Litinin, Talata da kuma Alhamis a tashoshi bakwai na Gidajen Rediyon Vision Media Services da ke fadin Najeriya.

Tattaunawar wannan shiri ta ta’allaka ne a kan harkokin gwamnati da yadda gwamnati ke kashe kudi ciki har da bin diddigin tanade-tanaden da kasafin kudin kasar ya yi da kuma sauran batutuwa da suka shafi matsalar tsaro da ta addabi kasar.

To sai dai a cewar Shu’aibu Mungadi, daya daga cikin manyan mahukuntan kafar ta VISION da Farin Wata, hakan bai zo masu da mamaki ba ganin yadda shirin ke bankado kura-kuran gwamnati kuma ga lokacin babban zaben kasar na karatowa.

A zantawarsa da Muryar Amurka, Shu’aibu Mungadi ya ce “Toh alal hakika ba mu yi mamaki ba, saboda mun san an dade ana kokarin yi mana bita-da-kulli, don muna ganin wani hadin baki ne aka yi domin a rufe wannan shiri don ko banza ana daf da fara al’amuran zabe a kasar.

“Kuma a zamanin Jonathan wannan shiri ya yi ta tona asirin gwamnatinsa wanda ya sa ’yan kasa suka raja’a ga wannan jam’iyya mai ci ta APC a yau.

“Saboda haka su na ganin kamar za a maimaita abin da ya faru can baya tun da dai ’yan kasa suna ganin abin da ke faruwa da abubuwan da ake yi ba daidai ba a wannan gwamnati musamman kasawar da aka yi ta kawo tsaro, kasawar da aka yi ta yaki da cin hanci da rashawa da kasawar da aka yi ta farfado da tattalin arziki yan kasa na cikin ukuba.

Idan ana iya tunawa, ko a shekarar 2014 sai da gwamnatin tsohon shugaba Goodluck Jonathan ta hana gidan radiyon gabatar da shirin, wanda matakin gwamnati mai mulki na yanzu ke nufin sau biyu kenan ana daukar irin wannan mataki kan gidan rediyon, na dakatar da shirin tsawon wata shida tare kuma da cin tarar hukumar rediyon naira miliyan biyar.