✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Dalilin da ake min kallon aljani —Abin Al’ajabin Falakin Gombe

Abin Al’ajabin Falakin Gombe ya ce yana so ya zama malamin jami'a

Kimanin mako biyu da suka gabata ne aka rika yada wasu hotunan wani wada a kan doki a lokacin bikin Hawan Sallah a Gombe fadar Jihar Gombe, inda aka rika kiran sa da Abin Al’ajabin Falakin Gombe wanda kuma shigarsa ta dauki hankalin jama’a har hakan ya sa wadansu suke yi masa ganin kamar aljani ne ba mutum ba.

Ganin yadda kafafen sadarwar zamani suke ci gaba da yayata cewa wannan mutum ya bar duniyar nan ya koma duniyarsu ce, ya sa Aminiya ta zakulo shi domin zantawa da shi game da rayuwarsa da kuma jin me ya sa ake yin wadannan surutai a kansa:

Abun Al’ajabin Falakin Gombe sunansa Abdurrazak Abubakar, kuma dan kabilar Waja ne daga garin Kulani da ke Karamar Hukumar Balanga a Jihar Gombe.

Amma yaan zaune ne da mahaifinsa a Unguwar Tumfure kafin ya koma gidan Falakin Gombe da ke Unguwar Turawa (GRA).

Ya shaida wa Aminiya yadda aka yi hawansa ta burge mutane a lokacin bikin Karamar Sallah da cewa ya kasance wada ne kuma ya yi shiga ta ban-mamaki da ta dauki hankalin masu kallo kuma ba ko’ina ne ake samun wada ya hau doki haka ba.

Abdurrazak Abubakar, ya ce dukkan kayayyakin da ya yi hawan Sallah da su Falakin Gombe Alhaji Kabiru Tsoho ne ya samar masa da su don ya kara inganta shi ya burge mutane a ce ayarin Falaki ta burge mutane.

– Batun duniyar da ya fito

A wata hira da aka yi da shi a wani bidiyo, ya nuna cewa zai koma duniyarsu, tosai dai Abin Al’ajabin Falakin Gomben ya ce ya fadi haka ne saboda wadansu ba su yarda shi mutum ba ne kuma sai ya bi su a haka, ya ce zai koma duniyarsu.

“Amma ba ni da wata duniya ta daban da ta mutane, ni ma mutum ne kamar kowa,” inji shi.

Ya ce ganin yanzu babu inda hotonsa bai je ba, hakan ya sa ya yi sanu kuma yana da burin idan ya girma ya zama mai taimakon al’umma.

Abun Al’ajabin Falakin Gomben ya ce, “Idan Allah Ya kai mu Babbar Sallar Layya,” Yana shiri na musamman don ganin ya kara burge mutane fiye da yanzu domin fitar da zai sake yi, za a ga kamar da gaske ba mutum ba ne.

Ya ce ba wannan ne hawan Sallah na farko da ya yi ba, amma shigar tasa ce ta sa ya fito fili aka gan shi inda cikin dubban mutane ya zama abin nunawa.

Sai ya ja hankalin mutanen da suke da wata nakasa cewa kada su ga don Allah Ya yi su da wata nakasa su dauka cewa ba su da yadda za su yi a rayuwa, maimakon haka su tashi su yi duk abin da za su iya, Allah Zai taimake su kamar yadda shi ma da yake wada, Allah Ya nuna shi a duniya cikin lokaci kadan.

Abin Al’ajabin Falakin Gomben ya ce yana karatu kuma Falakin Gombe ya dauki nauyin karatunsa daga yanzu har zuwa jami’a, kuma ya ce idan ya gama jami’a ya zama malami nan ma zai kara zama abin al’ajabi.

Daga nan sai ya yi amfani da wannan damar ya yaba wa Mai Martaba Sarkin Gombe, Alhaji Abubakar Shehu Abubakar III, kan yadda ya zakulo mutanen da ba sa kyamar jama’a irin su Alhaji Kabiru Tsoho, ya ba su sarautu da har ya shiga ayarinsa duniya ta san shi.

Kuma ya kara gode wa Mai Martaba Sarkin Gombe kan yadda yake yi wa marasa galihu na cikin al’umma alheri yana taimaka musu a watan azumi da kayan abinci da tufafi.