✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Dalilin da ake samun koma-bayan kwallon kafa a Najeriya – Kofar Mata

Bello Musa Kofar Mata sananne ne a harkar kwallon kafa.  Ya yi wasa a kulob da dama a Najeriya amma ya fi shahara a kulob…

Bello Musa Kofar Mata sananne ne a harkar kwallon kafa.  Ya yi wasa a kulob da dama a Najeriya amma ya fi shahara a kulob din Kano Pillars. Ya taba buga wa kungiyoyin kwallon kafa na kasa da suka hada da Super Eagles da U-17 da kuma U-20. Aminiya ta zanta da shi inda ya bayyana tarihinsa  da irin kalubalen da ya fuskanta da kuma dalilin da ya sa ake samun koma-baya a harkar kwallon kafa a Najeriya:

Mene ne tarihinka a takaice?

Sunana Bello Musa Kofar Mata.  An haife ni a Kofar Mata a Karamar Hukumar Birnin Kano a Jihar Kano. Na yi firamare da na sakandare  a Kofar Nasarawa Special Primary And Secondary School.  Bayan na kammala ne sai na yi Diploma (ND) a Kwalejin Kimiyya da Kere-Kere ta Jihar Kano, daga nan na shiga harkar kwallon kafa, kuma Allah Ya taimaka na samu daukaka a ciki. Tunda a cikinta nake ci, nake  sha sannan nake taimakon ’yan uwa da abokan arziki.

Wadanne kungiyoyin kwallon kafa ka taba yi wa kwallo?

Kulob di na na farko a matakin sakandare shi ne Buffalo, wanda daga nan na buga gasar cin Kofin Duniya na Makarantun Sakandare a kasar Faransa, kuma a wannan gasar na zama wanda ya fi kowa  yawan zura kwallaye a raga har aka ba ni kyautar Takalmin Zinare, wanda har yanzu idan na kalle shi ina alfahari. Daga nan ne kulob din Kano Pillars suka dauke ni.   Daga Pillars sai na je kungiyar Heartland da ke Owerri, sannan sai na sake komawa Kano Pillars.   Daga nan sai na je kungiyar  Ifeanyi Uba na yi shekara daya daga nan ne na koma kungiyar kwallon kafa ta El-Kanemi Warriors da ke Maiduguri inda yanzu na yi shekara uku tare da su.

Ko ka taba buga wa wata kungiyar kwallon kafa a kasar waje?

Ban taba buga wa wata kungiya ba a waje, amma kusan duk wata kasa da ka sani a Turai na je kuma na yi wasa a matakin neman kulob. An kai ni kasar Norway ni da wani abokina wanda ya buga wa Niger Tornadoes wato Solomon Owello, inda daga karshe suka dauki Solo suka ce wai ni na yi musu tsada daga nan na wuce kasar Holland bayan wasu kwanaki kuma muka wuce kasar Beljiyam a can ma ba mu daidaita ba, sai Manajana ya wuce da ni kasar Austireliya inda na yi atisaye da wata kungiya na wani dan lokaci shi ma dai ban san yadda abin ya kasance ba, ba su dauke ni ba. A haka kuma ban dawo gida ba sai muka wuce kasar Slobakiya, a can ina zuwa wata karamar kungiya ta dauke ni ba tare da bata lokaci ba. Amma da na dubi kudin da suka ba ni sai na ga kudin da nake karba a Kano Pillars ya fi abin da za su ba ni nesa ba kusa ba, don haka sai na fada musu ban amince ba, nan take aka soke kwangilar. Daga nan duk da yake ya nemi mu wuce wata kasar ni kuma sai na yi gajin hakuri na dawo Najeriya.

Wadanne nasarori ka samu a harkar kwallo?

A nemi Jaridar AMINIYA don samun cikakken rahoton.