✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Dalilin rashin rikicin addini ko kabilanci a Kano —Ganduje

Za a rika gudanar da taron addu’o’i duk shekara a Jihar Kano.

Gwamna Abdullahi Umar Ganduje ya bayyana cewa ba a samun matsalolin da suka danganci rikicin addini ko kabilanci a jiharsa a sakamakon addu’o’in da ake kwararawa ba dare ba rana.

Ganduje ya ce baya ga adduoin da ke sanya mutanen Kano shamakin mugun ji da mugun gani, wannan zaman lafiya da ya wanzu a jihar yana da kuma da alaka ne da hadin kan da ake samu a tsakanin jami’an tsaro.

Gwamnan wanda ake yi wa lakabi da Khadimul Islama, ya bayyana hakan ne a Filin Wasa na Sani Abacha, inda a nan ne aka gudanar da taron addu’o’in samun zaman lafiya da kuma tsaro na Kasa a ranar Asabar.

Ganduje ya kuma bukaci jigo na Darikar Tijjaniya a Najeriya, Sheikh Dahiru Usman Bauch, wanda yana daga cikin manyan malaman addinin Islama da suka halarci taron, da ya shirya taron bikin Maulidin Sheikh Ibrahim Nyass na gaba da za a gudanar a Jihar Kano.

Ganduje tare da Sheikh Dahiru Bauchi a filin wasa na Sani Abacha

Da yake jawabi a taron, Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya ce yaki da matsalar tsaro da sauran kalubalen da suka addabi Najeriya suna bukatar a nemi dauki daga Allah Buwayi Gagara Misali, wanda hakan ne zai rubanya kwazon da kuma tashi-tsayen da gwamnatin Tarayya ta yi na tunkarar lamarin.

Ganduje ya yi wa Shugaba Buhari godiya dangane da kokarinsa na ganin an samu wanzuwar zaman lafiya da tsaro, duk da cewa Allah Madaukakin Sarki kadai ne zai iya tabbatar da hakan, lamarin da ya ce gudanar da addu’o’i da rokon ya yi mana ludufi ita kadai ce mafita.

A kan haka ne Ganduje ya bayar da tabbacin cewa za a rika gudanar da taron addu’o’i duk shekara a Jihar Kano.

Buhari, wanda Karamin Ministan Noma Mustapha Baba Shehuri ya wakilta, ya ce gwamnatinsa ba ta yi ba kuma ba za ta yi kasa a gwiwa ba a kokarin da take yi na dawo da zaman lafiya da tsaro a kasar nan.

Kazalika, Buhari ya yaba wa Ganduje dangane da matakan da ya shimfida a fafutikar da yake yi domin wanzar da zaman lafiya a kasar ta hanyar shirya taron addu’o’i.

Ya kuma yi kira ga daukacin al’ummar Jihar Kano da su ci gaba da mara wa Gwamnatin Ganduje baya, inda ya buga misali da cewa manyan ayyukan ci gaba da ya assasa a jihar ba za su tabbata sai a wuri da kuma lokaci da zaman lafiya ya wanzu.