✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Dalilin da Buhari ya gaza cika alkawuransa –Bashir Tofa

‘A dauki barazanar Asari Dokubo da muhimmanci’

Dan takarar Shugaban Kasa a karkashin Jam’iyyar NRC a zaben 12 ga Yunin 1993 da aka soke Alhaji Bashir Othman Tofa ya fede biri har wutsiya kan rashin cika alkawuran da Shugaba Buhari ya.

Ya kuma yi wa Aminiya bayani kan matsalar rashin tsaro da a nuna kyama da ake yi ga Fulani musamman a Kudancin Najeriya da kuma martanin da Gwamnatin Tarayya ta mayar ga ayyana kafa gwamnatin Biyafara da Asari Dokubo ya yi.

Sauran muhimman maganganusa sun shafi cece-ku-ce kan zaben Shugaban Kasa na 2023, musamman batun karba-karba da samar da ’yan takarar Shugaban Kasa da Mataimakinsa mabiya addini da sauransu kamar haka:

 

Matsalar tsaro tana karuwa musamman ganin har yanzu Boko Haram na barna a Arewa maso Gabas, yayin da ta’asar ’yan bindiga da masu garkuwa da mutane ke yaduwa a Arewa maso Yamma, baya ga ta’asar sauran miyagu a sauran sassan. Me za a yi a magance haka?

Hakika muna cikin tsaka-mai-wuya da rashin alkibla a kasar nan. A shekarun baya in ka ce za a iya samun irin abubuwan da suke faruwa, jami’an tsaro na SSS ba za su dauki lamarin da wasa ba.

Sai dai komai yana da dalilinsa. Daya daga cikin gazawarmu a matsayin al’umma ko gwamnati shi ne mun kasa yin dogon bincike mu gano dalilan mutanen da suke yin abubuwan nan, don haka aka kasa gano hanyar da ta dace a bi, don a yi gyara.

Kawai muna kiran mutane ’yan ta’adda ko mashaya ko barayi da sauransu ba tare da binciko dalilin da suke wadannan abubuwa ba. Har yanzu mun kasa gano dalilin da Boko Haram ko ’yan bindiga suke yi mana ta’asa ko wane ne ke tallafa musu kuma a kan me?

Akwai bukatar mu waiwaya baya mu gano haka. Sai mun san dalilin ne kawai za mu yanke shawarar hanyar da ta fi dacewa wajen magance lamarin a dawo da zaman lafiya a kasa.

Idan muka koma baya ga tambayarmu, zan iya cewa na daya: an fi kai wa yara ’yan makaranta hari ne saboda hakan ne mafi jawo a tausaya musu. Kuma hakan na haifar da bukatar daukar matakin gaggawa saboda matsin da iyaye da sauran jama’a ke yi. Kuma tunda galibin iyayen matalauta ne, makarantun suna karkashin hukumomin ilimi na gwamnati, to gwamnati ce za ta dauki nauyin biyan kudin fansar da ake nema.

Sannan tunda akwai dimbin almundahana a kusan komai a Najeriya, ba za a kawar da zargin cewa wadansu jami’an gwamnati na amfani da wannan dama ta biyan kudin fansa su samu kasonsu, don haka suke tabbatar da an hanzarta biyan. Kamar dai a yi wa banki fashin Naira miliyan 10 ne, wadansu manyan jami’ansa su bayar da rahoton an yi fashin Naira miliyan 30.

Rufe kusan makarantu 450 a yanzu wata babbar nasara ce ga Boko Haram; duk da tana yiwuwa kai-tsaye ba su ne suke garkuwa da daliban ba.

Hadarin wannan lamari shi ne idan ’yan bindigar da Boko Haram suka yi da’awar samun nasara, hakan na iya kusanto su, su ji akwai bukatar su yi aiki tare. Idan aka bari haka ta faru an gama da mu.

 

Kiraye-kirayen sake fasalin kasa na dada karbuwa. Mene ne ra’ayinka kuma ta yaya kake ganin za mu magance batutuwan da suka shafi haka?

Ni ne Shugaban Kungiyar Abokan Dimokuradiyya; wata karamar kungiya ta masu kishin Arewa da suke kokarin gani da auna komai da bukatun kasa.

An yayata matsayarmu sosai kan sake fasalin kasa, kuma yanzu yana gaban Majalisar Dokoki ta Kasa. Wadanda suke sha’awa suna iya duba ta. Ba ni da wani ra’ayin sabanin wancan. Abin da zan kara shi ne ra’ayoyin da na karanta wasu an rubuta su ne da munanan manufofi ba bukatun kasa ba.

 

Wadanne manyan abubuwa biyu kake jin ya kamata a gyara a tsarin mulkin 1999 don samar da kyakkyawan shugabanci?

Rage kudin gudanar da gwamnati da jerin abubuwan nan uku.

 

Yaki da almundahana da rashin tsaro da matsalar tattalin arziki su ne manyan manufofin wannan gwamnati. Yaya za ka auna Shugaba Buhari kan wadannan?

Zan maimaita abin da na dade ina fadi. Shugaban Kasa ya rasa abokan tafiyar da yake nema su yi wadannan abubuwa da ya yi alkawari. Kuma idan ba mataimaka na kwarai, haka za a ci gaba da dora masa laifi.

Abin da nake tunani shi ne, idan ya sanya hannu a kan abu da yake da yakinin zai amfani kasa, sai kawai ya dauka za a aiwatar da shi kamar yadda ya yi umarni.

Akwai alamun babu tsarin bibiya ko bincike, ko kuma koyaushe ana gaya masa al’amura na tafiya kamar yadda aka tsara sai ya yarda hakan gaskiya ne.

Ni a yanzu haka addu’a nake yi masa ina rokon Allah Madaukaki Ya taimake shi da ingantacciyar lafiya da sakakkiyar zuciya don ya rika gani tare da aiki da gaskiya. Lokaci yana kure masa. Zuwa badi zai zamo bai da katabus.

 

An fara cece-ku-ce kan zaben Shugaban Kasa na 2023. Mene ne tunaninka game da makomar Najeriya a 2023?

Na farko mu fara tabbatar da kasarmu ta tsira; ba kawai a hade ba, har da zaman lafiyar da muke nema domin bayar da damar a yi zaben cikin nasara a 2023. Kasar nan ta rarrabu sosai a yanzu ana ta samun ra’ayoyin banza da nuna kyama marar dalili.

Na biyu, ban taba goyon bayan yin karba-karba a komai ba. Ba hakan ya saba wa dimokuradiyya kadai ba ne, zai ma hana mu rika jin mu ’yan Najeriya ne ko kuma za mu zabi “Shugaban Najeriya ne.”

Sai yaushe ne za mu daina daukar kanmu ’yan Arewa ko ’yan Kudu? Ban sani ba. Kuma zai yi wuya mutanen Kudu su zauna su cimma matsaya a bar wa daya daga cikin shiyyoyinsu uku. Zai yi kyau su kwatanta hakan don nuna cewa Kudu daya ce. Dan takararsu sai ya fuskanci ’yan takara da dama da Arewa ta fitar a daya ko fiye daga cikin jam’iyyun siyasa.

Hakika ina ganin batun tura shugabanci ga shiyya-shiyya abu ne da ke cutar da dimokuradiyya da hadin kan kasar nan.

Alama ce ta koma baya, a rika ci gaba da farfagandar rarraba kan kasa kan batun shugabanci, maimakon a samar da wanda zai yi wa dukkan ’yan Najeriya hidima bisa daidaito da adalci.

Jam’iyyar PDP ce ta fara wannan wautar. Sun bata tsarin siyasar kasar nan amma suna tunanin shi ne abin da ya fi dacewa. Yanzu ga shi ya zamo abin da zai iya wargaza kasar nan in ba a yi taka-tsantsan ba, Allah Ya kiyaye!

 

Yayin da ake tunkarar zaben 2023, wadansu sun fara kawo batun tikitin Musulmi-zalla ko Kirista-zalla kamar yadda Jam’iyyar SDP ta yi a zaben 1993. Suna ganin hakan zai magance rarrabuwar kan da ake fuskanta. Kana ganin wannan tikiti zai iya samun amincewar ’yan Najeriya?

Kasar nan ta yi muguwar rarrabuwar da ba wata jam’iyya da za ta yi gigin bayar da tikiti ga Musulmi-zalla ko Kirista-zalla.

Ina fata wata rana a yi watsi da kabilanci da bambancin addini a harkokin siyasarmu.

 

Kungiyar Masu Ruwa-daTsaki ta Kano (KCCI), da kake shugabanta ana mata kallon ta siyasa ce. An sa ran za ka motsa a zaben 2019, amma sai wadansu suka ce ba ka shirya ba ne. Yanzu ga zaben 2023 ya taho, a matsayinka na tsohuwar zuma me kake ciki?

Kungiyar KCCI, an kafa ta ce don tabbatar da kare bukatun dukkan mutanen Kano da wadanda suke zaune a cikinta ta hanyar zaman lafiya da dabaru da suka mai ma’ana.

Mu ba kungiyar siyasa ba ce, amma mun damu da wa yake shugabantarmu. Ba ruwan KCC da neman wani mukamin siyasa.

Idan ina da burin haka, ban fada wa kowa ba, kuma ko da zan nema a wata rana to ba a nan Kano ba.

A yanzu ba ni da wannan buri. Na bar komai a hannun Allah, Shi Ya san abin da ya fi dacewa da ni.

Don haka ba ni da wata damuwa a wannan bangare. Duk abin da zan yi a siysance nakan yi shi ne bisa gaskiya da cikakkiyar kare bukatun Najeriya da mutanenta a zuciya.

 

A bara Kano ta rasa fitattun ’ya’yanta maza da mata, inda wadansu ke cewa sun bar gibin da ba za a iya cikewa ba. Me za mu yi don maye gurbin wadansu daga cikinsu?

Babu abin da ba za a iya maye shi ba. Har yanzu muna da shugabanni na kwarai, kuma muna girmama wadanda suka girme mana. Wannan na daga cikin al’adunmu.

Duk muna sane da cewa lokaci na canjawa, kuma wasu al’adu sun samu zama a nan kuma za su ci gaba da zama.

Muna kokari sosai mu kwaikwayi masu kyansu, kuma mu yi kokarin koya musu mafiya kyan namu.

 

Alamu sun nuna babu wanda ake saurare a Kano; misali rikicin Masarautar Kano da sauran batutuwan da dattawa suka gaza magancewa. Shin dattawan ba su da tasiri ke nan a yanzu?

Ba gazawar dattawa ba ne da suka nuna damuwa kan wasu al’amura na yunkurin rusa harkokin sarauta a Jihar Kano, sai dai a ce gazawar shugabannin siyasa da suka fito gadan-gadan su rusa abin da aka gina kuma aka gada shekara dubu ko fiye. Kuma abin da siyasa ta rusa, siyasa za ta sake ginawa da yardar Allah.

 

A matsayinka na jagoran ’yan bokon Kano, ana ganin yanzu kana jagorantar “adawa” da Gwamna Ganduje, musamman bayan ya kekketa Masarautar Kano; inda kuka kai shi kotu sau dama. Kuma gwamnatin jihar ta sake samun kanta a tsaka-mai-wuya kan yadda take kula da kayayyakin tarihi da muhimman kadarorin jihar, gidan zoo da lambun bincike ana zargin za a sayar da su. Mene ne ra’ayinka?

Ni ba makiyin Gwamna Ganduje ba ne. Ba ya bukatar makiya. Ina kokari ne in yi amfani da dan karamin lokacin da nake da shi in yi wasu abubuwa masu kyau.

Ba ni da lokacin yin gaba da wani ko bata aikin wani ko jiha. Muna ci gaba da yin addu’a ga Gwamna Ganduje kan Allah Ya yi masa jagora kafin karshen wa’adinsa domin shi, ko wani babu wanda ya san abin da zai zo gaba.

 

A Kudu maso Yamma, ana takura wa Fulani makiyaya kan laifin wadansu kalilan daga cikinsu. Shin Gwamnatin Tarayya da na jihohi sun tafiyar da lamarin yadda ya dace?

Hakika abin da ke faruwa a kasar nan abin kunya ne. Kuma mafi muni, kalilan din gwamnonin Kudu sun gaza bisa dalilin da ba mu sani ba, kan su dakatar da kisan gillar; a Najeriya ta yanzu, wannan kisan rashin imani na aukuwa da mutanen da suke zaune ne a wadancan jihohi. Idan akwai miyagu ko su wane ne, doka ce ya kamata ta yi aiki a kansu, ba ’yan daba su rika auka musu ba.

Sannan bai kamata mu gwama mutanen kirki da na banza ba. Akasarin Fulani mutanen kirki ne kamar yadda akasarin mutanen Kudu suke. Wannan ya sa muka yi kiran a yi taka-tsantsan a nan Arewa, kuma mutane sun ji sun yarda da mu. Bai kamata mu bari wadansu kidahumai, miyagun mutane su jefa kasar nan a matsalar da za ta jawo mugun abin kaico ba.

Duk da haka bidiyo suna ci gaba da fitowa daga Kudu na sababbin kashe-kashen mutane da dabbobi da kone dukiyoyi.

Gwamnatin Tarayya ta ki cewa komai kan wadannan kashe-kashe; haka manyan shugabannin da muka sani kuma muka zama kamar danginsu a can Kudu.

Hakika da zafi ta yadda mutum zai iya tunanin cewa suna goyon bayan abin da ake yi ko suna da raunin da za su kira wadannan mutane su daina abin da suke yi.

Idan irin wadannan abubuwa suka ci gaba, za a fara tattauna batun neman diyyar rayuwa da dukiyar da aka kashe ko aka lalata a wani wurin.

Muna fata za a dauki wannan da matukar muhimmanci a magance shi bisa adalci. In ba haka ba, wata matsalar na iya tasowa.

 

A farkon makon jiya Asari Dokubo ya ayyana kafa gwamnatin Biyafara, amma sai Gwamnatin Tarayya ta mayar da batun abin ba’a. Shin ya kamata ’yan Najeriya su nuna damuwa da wannan batu na bayan nan?

Marasa wayo na iya daukar Alhaji Asari Dokubo a matsayin dan kama. To amma me zai faru idan kalamansa suka zamo sanya dan ba ne na wani babban shiri?

Bai kamata a dauki barazana ga kasar nan abin wasa ba. In da wani ne daga Arewa ya fadi kadan daga abin da Alhaji Dokubo ya fada, da tuni jami’an tsaro sun kama shi, saboda sun fi samun saukin musguna wa ’yan Arewa.

Ina mamakin yadda hakan ke aukuwa. Mai yiwuwa saboda ba mu cara ne, ba mu buga kasa, mu ce kasar za ta wargaje. Shi ya sa muka bari ana ci mana zarafi ba tare da dalili ba.