✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

‘Dalilin da buhun wake ya kai N100,000 a Legas’

Abin da ya sa farashin ke kaiwa har N100,000 a kasuwannin Legas.

Shugaban Masu Sayar da Wake a Kasuwar Mil 12 da ke Legas, Alhaji Umar Muhammaed, ya ce a bana farashin wake ya yi tashin gwauron zabo, inda ya yi tsadar da ’yan kasuwa masu hadahadar waken ba su taba gani ba, inda ake sayar da buhun waken a kusan Naira dubu 100 a Legas.

Alhaji Umar Muhammed ya shaida wa Aminiya cewa, “A bana wake ya yi tsadar da ba a taba ganin irinsa ba a baya, inda ake sayar da buhun waken dan Maiduguri a kan Naira dubu 75 zuwa dubu 80 ta yadda in an cika babban buhun har kololuwa ana sayar da shi Naira dubu 100.”

Ya ce, dalilin tsadar waken shi ne karancin ruwan sama a bara da kuma barkewar cutar COVID-19 domin a sanadiyar cutar ce mawadata da jami’an gwamnati da kungiyoyin jinkai suka yi ta sayen kayan abinci suna raba wa jama’a a lokacin da ake cikin dokar kullen COVID-19.

“A wancan lokacin an sayi waken da manoma kan yi ajiyarsa domin irin wannan lokaci, wannan ne ya janyo karancinsa, kuma dama a ka’idar kasuwa duk abin da ya yi karanci za a ga farashinsa ya hau, wannan ne abin da ke faruwa domin karancin waken ne ya assasa tsadar.

“Haka kuma damina ba ta yi kyau ba, don haka bai wadata ba, wanda kuma aka samu an saye shi an raba wa jama’a sun cinye a lokacin kullen COVID-19,” inji shi.

Ya kara da cewa, “A baya kafin barkewar cutar, waken da ake kira Olutu a Legas wanda ake nomawa a Jihar Neja, buhunsa ba ya wuce Naira dubu 11 zuwa 12, amma a yanzu ya kai Naira dubu 70, sannan waken da ake kaiwa daga Maiduguri da ake kira Oloti Maiduguri shi ma buhunsa yana kaiwa Naira dubu 75.

“Sai dan uwansa da shi ma ake kaiwa daga Maiduguri da ake kira Oloyi Maiduguri, buhunsa karami yana kaiwa Naira dubu 40 zuwa 45.

“Akwai kuma farin wake da ake sayarwa buhu Naira dubu 45 zuwa 50, ya danganta da yanayin da aka samo shi a Arewa shi ma bai dade da zuwa ba wato sabo ne.

“Sai kuma yanzu da akwai sabon waken da ya iso kasuwa ba da jimawa ba, ana kiransa Oluwonda Oloyu Kwalebe, shi buhunsa Naira dubu 50 ake sayarwa; Zuwansa kasuwa ne ya sa farashin wake ya fara yin kasa a yanzu.”

Alhaji Umar ya ce, tsadar waken a bana a Legas wacce ita ce mafi muni a tarihi, buhun ya kai Naira dubu 75 zuwa 85.

“Amma maganar da ake yi cewa ya kai Naira dubu 100, ana iya samun haka ne idan ’yan kasuwa suka cika buhun har zuwa kololuwa suka yi masa kari.

“Ya ce tsadar waken ta sa abokan cinikinsu yawan korafi inda sau tari wanda ke iya sayen buhu guda a baya yanzu ba ya wuce ya sayi kashi daya bisa hudu na buhun, wanda sayen waken ya zame masu dole kuma suna da kudin saya,” inji shi.

Ya kuma ba da tabbacin cewa nan gaba kadan farashin waken zai sauka.