✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Dalilin da har yanzu nake jinyar tiyata a Landan – Tinubu

Tinubu ya ce yana dada murmurewa daga tiyatar kafar tasa.

Jagoran jam’iyyar APC na kasa, Bola Ahmed Tinubu ya ce har yanzu yana ci gaba da jinyar tiyatar da aka yi masa a kafarsa a birnin Landan.

Tsohon Gwamnan na Jihar Legas ya bayyana haka ne a lokacin da ya karbi bakuncin shugabannin Majalisar Wakilai da suka fito daga Arewacin Najeriya a birnin na Landan.

Sun kai masa ziyarar ne karkashin jagorancin Mataimakin Kakakin Majalisar Wakilai, Ahmed Idris Wase a ranar bikin cikar Najeriya shekara 61 da samun ’yancin kai [Juma’a].

Tinubu, wanda ya shafe kimanin wata uku a kasar ta Burtaniya, ya shaida musu cewa yana dada murmurewa.

Ya ce, “Cikin ikon Allah da kuma taimakon mutane irinku, ina dada samun sauki. Kawai dai tiyatar da aka yi  min ce dole sai ta dauki lokaci,” inji Tinubu.

Fitattun ’yan Najeriya da dama ne dai ciki har da Shugaban Kasa Muhammadu Buhari suka ziyarci Tinubun a inda yake jinyar a Landan.

Aminiya ta rawaito cewa ko a makon da ya gabata, an ga fastocin takarar Tinubu, wanda daya ne daga cikin masu sha’awar neman shugabancin Najeriya a 2023, a wasu tashoshin jiragen kasa na Landan.